Zan iya kada shugaba Buhari a watan Fabrairu mai kamawa - Kwankwaso

Zan iya kada shugaba Buhari a watan Fabrairu mai kamawa - Kwankwaso

- Zan iya kada shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Zan tabbatar da zaman lafiya, tsaro da ababen more rayuwa

- Siyasa ta jama'a ce, ina da sa'a da na fito daga jihar Kano

Zan iya kada shugaba Buhari a watan Fabrairu mai kamawa - Kwankwaso
Zan iya kada shugaba Buhari a watan Fabrairu mai kamawa - Kwankwaso
Asali: UGC

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma mai neman shugabancin kasa karkashin jam'iyyar PDP, Rabiu Musa Kwankwaso yace zai iya kada shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Yace zai tabbatar da zaman lafiya, tsaro da ababen more rayuwa Idan aka zabe shi a 2019. Yayi wannan bayanin ne a ranar juma'a, a tattaunawar da akayi dashi a Channels Television, inda yayi ikirarin yana da magoya bayan da zasu zabe shi a zaben fidda gwani na PDP.

"PDP a yanzu ta fi da. Idan aka ce wanene yafi cancanta, wa ke da karfin kayar da shugaban kasa gwamnatin nan, inda akwai zaman lafiya, cigaba, ababen more rayuwa da sauran su - toh a ra'ayi na, ana maganar Rabiu Kwankwaso ne " Yace.

"Siyasa fa kamar yanda kuka sani, ta mutane ce. Ina da sa'a ni Dan kano ne inda muka zama jihar da tafi kowacce jiha mutane a kidaya ta karshe da akayi kuma sanannen yanki."

"Muna da magoya baya da yawa, wadanda suka yarda damu kuma sun yarda indai mukayi nasara, suma zasuyi." Yace.

DUBA WANNAN: Yadda jarin kamfunna zasu kai tiriliyan a kasar nan

Kwankwaso wanda Sanata ne mai wakiltar Kano ta tsakiya, yace magoya bayan shi basu taba suna kamar yanda yanzu sukayi a kano da kuma Najeriya baki daya. Yace hakan ya biyo bayan nasarorin da ya samu lokacin da yake gwamnan jihar, ta bangaren ababen more rayuwa da ilimi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel