Badakalar N5.4bn: Sanata Adamu ya mayar wa gwamna Al-Makura kakausar martani

Badakalar N5.4bn: Sanata Adamu ya mayar wa gwamna Al-Makura kakausar martani

- Sanata Abdullahi Adamu ya mayar da martani kan kafa kwamitin bincike da gwamna Umaru Tanko Al-Makura ya yi domin bincikarsa

- Kwamitin mai mutane 10 zai yi bincike ne kan yadda gwamnatin Abdullahi Adamu tayi watsi da tashan wutan lantarki na Farin Ruwa da aka ware N5.4 biliyan domin aikin a jihar Nasarawa

- Sai da Sanatan Adamu wanda tsohon gwamna ne a jihar Nasarawa ya ce ko kadan kwamitin ba ta razana shi ba

A jiya, Alhamis ne sanata mai wakiltan yankin Nasarawa ta Yamma, Sanata Abdullahi Adamu ya ce ko kadan kwamitin bincike da gwamnan Nasarawa, Umaru Tanko Al-Makura ya kafa bata bashi tsoro ko kadan.

Vanguard ta ruwaito cewa Sanata Adamu ya yi wannan furucin ne yayin da ya ke mayar da martani kan kwamitin mutane 10 da Al-makura ya kafa domin bicika dalilin da yasa gwamnatin tsohon gwamna Adamu tayi watsi da aikin gina tsahar samar da lantarki na Farin Ruwa bayan kashe N5.4 biliyan.

Badakalar N5.4bn: Sanata Adamu ya mayar wa gwamna Al-Makura martani
Badakalar N5.4bn: Sanata Adamu ya mayar wa gwamna Al-Makura martani
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Wani mai kambun baka ya yi hasashen matsayin da APC da PDP za su tsinci kansu a zaben Osun

Legit.ng ta gano cewa Sanata Adamu ya bayar da wannan sanarwan ne a babban birnin tarayya, Abuja ta bakin mai magana da yawunsa, Alhaji Jibrin Abdullahi.

Sanatan ya ce yana maraba da kafa duk wata kwamiti da za ta bincike ayyukan da ya yi lokacin da ya ke gwamna a jihar ta Nasarawa.

Sanata Adamu ya ce dukkan abinda ya aikata lokacin yana gwamna anyi shi ne cikin tsari da biyaya ga doka kuma akwai shaidan da zai nuna hakan idan an bincika.

Hakan yasa Sanatan ya ce makirci ce kawai ta sharri da ake kokarin yi masa yasa gwamnan ya kafa wannan kwamitin domin gwamna Al-Makura ya samu cikaken bayani kan aikin tashan samar da lantarkin lokacin da Ministan Albarkatun ziyarci shi domin fada masa gwamnatin tarayya za ta karbi aikin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel