Wata sabuwa: Wani lauya ya maka Buhari, hafsoshin sojin Najeriya kotu

Wata sabuwa: Wani lauya ya maka Buhari, hafsoshin sojin Najeriya kotu

- Wani lauya ya maka Buhari, hafsoshin sojin Najeriya kotu

- Ya kai su kotu ne saboda shirin Atisayen rawar mesa na uku

- Hadda Buratai da Malami ya kai karar

Wani lauya dake ikirarin rajin kare hakkin bil'adama mai suna Mista Oleka Udenze dake zama a garin Abuja ya maka shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari da wasu mukarraban gwamnatin sa game da shirin Atisayen rawar mesa na uku watau Operation Python Dance 3 a turance.

Wata sabuwa: Wani lauya ya maka Buhari, hafsoshin sojin Najeriya kotu
Wata sabuwa: Wani lauya ya maka Buhari, hafsoshin sojin Najeriya kotu
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Wani gwamnan Arewa yayi magana game da batun komawar sa PDP

Shirin dai na 'Operation Python Dance' na zaman wani mataki da sojojin Najeriya suka dauka a watannin baya da nufin kakkabe dukkan wasu hatsabiban tsageru a yankin kudu maso gabashin Najeriya da ke son ballewa daga Najeriya.

Legit.ng ta samu cewa cikin mukarraban gwamnatin shugaban kasar da aka maka su kotun tare hadda ministan shari'a, Abubakar Malami, babban hafsan hafsoshin Najeriya Janar General Abayomi Gabriel Olanisakin da kuma hafsan sojin kasan Najeriya Laftanal Janar Tukur Buratai.

Shi dai lauyan ya kai karar ne da nufin kotun ta tursasawa wadanda yakai karar su janye batun su na kaddamar da Atisayen karo na uku da suke shirin yi a 'yan kwanakin nan.

A wani labarin kuma, Dakarun sojin Najeriya tuni sun soma aikin zuke tafkunan wasu garuruwa da kauyukan karamar hukumar Jos ta kudu dake a jihar Filato a cigaba da zurfafa binciken neman gawar dan uwan su da ya bace a kwanan baya.

A baya dai mun kawo maku labarin cewa wani babban jami'in rundunar sojin ta kasa mai suna Manjo Janar Idris Alkali ya bata a kan hanyar sa ta zuwa Bauchi daga garin Abuja.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel