Ashura: Yan shia sun yi arangama da jami’an tsaro a Potiskum 1 ya mutu 3 sun jikkata

Ashura: Yan shia sun yi arangama da jami’an tsaro a Potiskum 1 ya mutu 3 sun jikkata

Rahotanni sun tabbatar da mutuwar mutum daya wani karamin yaro a yayin da rikici ya kaure tsakanin yan shia da jami’an tsaron Najeriya dake jibge a garin Potiskum na jahar Yobe, inji rahoton jaridar the Nation.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito baya ga mutuwar karamin yaron, mabiya akidar shia guda uku sun samu munana rauni a sanadiyyar wannan arangama daya faru da misalin karfe 8 na safiyar Juma’a.

KU KARANTA: Kotun Najeriya ta daure wani dan kasuwa tsawon shekaru 140 a Kurkuku saboda laifin daya aikata

Kwamishinan Yansandan jahar, Sumonu Abdulmalik ne ya tabbatar da wannan lamari, inda yace: “Rikicin ya faro ne a daidai lokacin da mabiya El-Zakzaky suka fara gudanar da tattakinsu na Ashura, sai suka hadu da Sojoji inda suka yi kokarin kwace bindigar guda cikin Sojoji.

Ashura: Yan shia sun yi arangama da jami’an tsaro a Potiskum 1 ya mutu 3 sun jikkata
Yan shia
Asali: Depositphotos

“Daga nan ne fa sai taraliya ta barke, nan take Sojoji suka raunata mutane uku daga cikin yan shia, zan iya tabbatar faruwar wannan lamari, amma ina tsimayin samun karin rahotanni game da lamarin.” Inji shi.

Sai dai wani daga cikin shuwagabannin yan shi’an, Ibrahim El-Tafseer ya karyata maganan da kwamishinan Yansandan yayi, inda yace “Ba halin bane kwace makaman jami’an tsaro, maganan da kwamishinan Yansandan yayi ba gaskiya bane.

“Mun fi shekara 25 muna gudanar da tattakin ashura a Potiskum, amma a yau mun fito muna tattakinmu kwatsam sai Sojoji suka tare suka fara dukanmu, daga bisani kuma suka bude mana wuta, sun jikkata mutane uku, sun kashe mutum daya, amma ba daga cikinmu yake ba. Sa’annan sun kama guda daga cikinmusun tafi dashi.” Inji shi.

Wata majiya ta ruwaito cewa yan shian ne suka fara jefa duwatsu akan motocin rundunar jami’an tsaro ta hadaka, wanda hakan ne ya harzuka jami’an tsaron suka far musu. Amma dai kwamishinan Yansandan yace a yanzu hankula sun kwanta a garin Potiskum.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel