Kada wanda ya kula Saraki, a kyale shi ya ci gaba da babatun sa – Buhari

Kada wanda ya kula Saraki, a kyale shi ya ci gaba da babatun sa – Buhari

Fadar shugaban kasa ta roki magoya bayan Shugaban kasa Muhammadu Buhari da su yi watsai da lamarin Bukola Saraki, shugaban majalisar dattawa cewa kada su tanka wa masa kan babatu da suka da yake ta yi wa wannan gwamnati jaridar Premium Times ta ruwaito.

A cewar wata sanarwa dauke da sa hannun babban mai ba shugaban kasar shawara a harkokin labarai, Garba Shehu yace tun ada Saraki bai san da cewa Buhari ba zai iya ba a lokacin da suke tare yake yi masa kirari sai a yanzu.

Kada wanda ya kula Saraki, a kyale shi ya ci gaba da babatun sa – Buhari
Kada wanda ya kula Saraki, a kyale shi ya ci gaba da babatun sa – Buhari
Asali: Depositphotos

“Shi fa Saraki ya canja ne kawai domin yana neman tsayawa takarar shugaban kasa. Sannan kuma jam’iyyar da ya ke neman takarar a kai basu da abin cewa sai kawai ya maida hankali ga bata Shugaban kasar a idanun jama’a.

“Babu irin yaba wa Buhari da Saraki bai yi ba a baya-bayannan, Ya fadi da bakin sa cewa Buhari mutumin kirki ne, Buhari mutum ne mai cikakken lafiya, Salon mulkin sa ya cancanci yabo, duk ya fadi, amma da yake shima ya na so ya dare kujerar shugabancin Najeriya sai gashi tun kafin a kira assalatu, Saraki ya fara gaggawar nuna yunwar sa a fili.” Inji Garba Shehu.

Shehu ya roki magoya bayan shugaban kasar Buhari da kada su kula Saraki ballantana ma har su mayar masa da martani.

A wani labara na daban, Legit.ng ta rahoto cewa rundunar yan sanda sun tsaurara matakan tsaro kewaye da hedkwatar hukumar zabe mai zaman kanta dake Osogbo gabannin zaben gwamna da za’a gudanar a ranar Asabar, 22 ga watan Satumba a jihar.

KU KARANTA KUMA: APC na matakin karshe a kokarinta na kawo karshen rikice-rikice a jihohi APC na matakin karshe a kokarinta na kawo karshen rikice-rikice a jihohi

An zuba jami’an tsaro da yawa a ranar Alhamis, 21 ga watan Satumba yayinda hukumar ta fara rabon kayayyakin zabe ga ofishoshin INEC dake kananan hukumomi 30 na jihar.

Kwamishinan zabe na jihar Osun, Mista Olusegun Agbaje ya fadama majiyarmu akan wayar tarho cewa an raba kayayyakin zabe ga kananan hukumomi a shirin gabatar da zaben ranar Asabar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel