Zaben jihar Osun: Ban janye wa Omisore ba - Adeleke

Zaben jihar Osun: Ban janye wa Omisore ba - Adeleke

- Dan takarar gwamna na PDP, Sanata Adeleke ya ce baiyi yarjejeniyar janye wa kowa ba

- Sanata Adeleke ya yi kira ga magoya bayansa suyi watsi da jita-jitar cewa ya janyewa Iyiola Omisore

- Adeleke kuma ya karyata rahotannin da ke cewa ya gana da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo

Dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a zaben jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke ya ce babu kanshin gaskiya cikin jita-jitar da ake yadawa na cewa ya janye daga takarar ya barwa Sanata Iyiola Omisore na jam'iyyar SDP.

Zaben jihar Osun: Ban janye wa Omisore ba - Adeleke
Zaben jihar Osun: Ban janye wa Omisore ba - Adeleke
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Wani mai kambun baka ya yi hasashen matsayin da APC da PDP za su tsinci kansu a zaben Osun

A sanarwar da ya fitar ta bakin mai magana da yawunsa, Malam Olawale Rasheed a yau Juma'a, dan takarar gwamnan na PDP ya ce yana nan daram bai janye ba kuma za'a fafata da shi a zaben da za'a gudanar gobe Asabar.

Sanarwan ta ce, "Ademola bai janye wa kowa ba, har yanzu shine dan takarar gwamna a karkashin jam'iyyar PDP.

"Sanatan bai gana da tsohon shugaban kasa, Janar Olusegun Obasanjo ba ko kuma Sanata Iyiola Omisore. Bai yi wata yarjejeniya da kowa ba.

"Sanata Adeleke shine dan takarar jam'iyyar PDP saboda haka ina kira ga masu jefa kuri'a suyi watsi da labaran bogi da ke yaduwa cewa Adeleke ya yi yarjejeniya da SDP ko ADP. Jam'iyyar PDP ta shiga takarar ne domin tayi nasara", Inji Olawale.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel