Cutar kwalara ta bulla jihar Yobe, ta kashe mutane 61 - Kwamishinan lafiya

Cutar kwalara ta bulla jihar Yobe, ta kashe mutane 61 - Kwamishinan lafiya

- Gwamnatin jihar Yobe ta tabbatar da bullar cutar kwalara a jikin mutane 906, inda cutar tayi ajalin mutane 61

- Wasu daga cikin rahotannin AWD da aka samu sun nuna cewa kwayar halittar Vibrio bacteria ne, kwayar halittar da ke kawo cutar kwalara

- An yi kira ga shuwagabannin addinai dana gargajiya da su wayar da kan jama'a akan hanyoyin dakile yaduwar cutar

Gwamnatin jihar Yobe a ranar Juma'a 21 ga watan Satumba, ta tabbatar da bullar cutar kwalara a jikin mutane 906, inda cutar tayi ajalin mutane 61 ya yin da har yanzu sauran mutane 50 ke kwance a asibitoci da ke a fadin jihar don basu kulawar likita.

Dr. Muhammad Kawuwa, kwamishinan lafiya na jihar ya bayyana hakan a cikin wata sanar a Damaturu, yana mai cewa an samu rahotonnin amai da gudawa sakamakon gurbataccen ruwan sha a sassa na jihar, sai dai bayan gudanar da bincike a dakin binciken cutuka da gano maganinsu, an gano cewa cutar kwalara ce mai tsanani.

"Wasu daga cikin rahotannin AWD da aka samu sun nuna cewa kwayoyin Vibrio bacteria ne, kwayar cutar da ke kawo kwalara," a cewar kwamishinan.

KARANTA WANNAN: Fadar shugaban kasa ta roki magoya bayan Buhari da su yi biris da kalaman Saraki

Cutar kwalara ta bulla jihar Yobe, ta kashe mutane 61 - Kwamishinan lafiya
Cutar kwalara ta bulla jihar Yobe, ta kashe mutane 61 - Kwamishinan lafiya
Asali: Facebook

A cewar sa, an samu rahoton bulluwar cutar a jikin mutane 906 a cikin kananan hukumomi 6 da ke jihar da suka hada da; Gujba, Gulani, Damaturu, Fune, Potiskum da kuma Nangere, a cikin watanni biyu.

"Sama da masu dauke da cutar 795 ne aka yiwa magani cikin nasara, sai dai har yanzu akwai mutane 50 daga cikinsu da ke kwance a asibitocin da ke fadin jihar."

Kawuwa ya ce ma'aikatar lafiya tare da hadin guiwar hukumar lafiya ta duniya WHO, asibitin koyarwa na jami'ar Maiduguri da kuma cibiyar dakile yaduwar cutuka da ke Abuja, na ci gaba da bincike don gano hanyoyin yaduwar cutar da magance su.

KARANTA WANNAN: Kiwon lafiya: Rundunar sojin sama ta kai daukin gaggawa ga al'umar Zangeru, jihar Niger

Ya ce wannan na daga cikin yunkuri da jihar ta ke yi don dakile yaduwar cutar da kuma nemo tallafi daga sauran kasashen ketare da ke baiwa kasashe dauki wajen dakile yaduwar ire iren cutukan.

Kwamishinan ya bayyana rashin tsaftar muhalli, rashin wuraren ba-haya da zubar da shara hadi da ruwan ambaliya a matsayin dalilan da suka jawo bulluwar cutar, yana mai kira ga kungiyoyin tsaftace ruwan sha, shuwagabannin addinai dana gargajiya da su tallafawa gwamnati wajen wayar da kan jama'a akan hanyoyin dakile yaduwar cutar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Zaben Osun: INEC ba ta hana amfani da wayoyin salula a rumfunan zabe ba | Legit.ng TV

Asali: Legit.ng

Online view pixel