Sanata Stella Oduah ta sake sauye-sheka bayan ta lura kujerar ta na rawa

Sanata Stella Oduah ta sake sauye-sheka bayan ta lura kujerar ta na rawa

Mun ji labari cewa Sanata Stella Oduah ta dawo babbar Jam’iyyar adawa ta PDP bayan ta fice daga Jam’iyyar kwanaki. Yanzu dai Sanatar ta Anambra tayi watsi da Jam’iyyar APGA da ta koma a da.

Sanata Stella Oduah ta sake sauye-sheka bayan ta lura kujerar ta na rawa
Tsohuwar Ministar Jonathan Stella Oduah za ta sake takarar Sanata a PDP
Asali: Facebook

Sanata Stella Oduah tayi watanni 4 ne kacal a Jam’iyyar APGA sai tayi maza ta sake sauya sheka zuwa PDP bayan ta lura da cewa Gwamnan Jihar Anambra Willie Obiano yana neman tsaida wani ‘Dan takarar Sanata a APGA.

Kamar yadda labari ya zo mana, tsohuwar Minista Sanata Oduah tayi wuf ta tsere daga APGA ta dawo Jam’iyyar PDP bayan da ta fahimci cewa ba za ta samu tikitin Jam’iyyar a 2019 domin komawa kujerar Sanatan ta ba.

KU KARANTA: Jerin sunayen Sanatocin APC da suka rage bayan ficewar wasu

Jama’a dai sun yi mamaki da su ka ga Sanatar ta Anambra ta Arewa wajen tantance ‘Yan takarar PDP bayan ta tsere daga Jam'iyyar a farkon shekarar nan. Yanzu dai wani tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar ne ke neman kujerar ta.

Prince Chinedu Emeka ya yanki fam a Jam’iyyar APGA domin karawa da tsohuwar Ministar kasar. Hakan ya sa ta koma PDP domin kuwa Gwamna Obiano yana tare da ‘Dan takarar. Oduah dai tana da Jama’a Yankin Anambra.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel