Gwamnatin tarayya ta ware kudi na mussaman domin karya farashin shinkafa yar gida

Gwamnatin tarayya ta ware kudi na mussaman domin karya farashin shinkafa yar gida

Gwamnatin tarayya a ranar Alhamis, 20 ga watan Satumba ta bayyana cewa ta ware kudi na mussaman domin tallafawa manoman shinkafa don ganin an karya farashin shinkafa yar gida.

Ministan gona da raya karkara, Cif Audu Ogbeh yace bankin noma da ma’aikatar ne zasu kula da kudin inda ya kara da cewa gwamnati tayi wannan karamcin ne domin tabbatar da cewar shinkafa yar gida tayi araha sannan kuma tafi shinkafa yar waje farin jini a kasuwa.

Yayi Magana ne a lokacin wani taro na kungiyar manoman shinkafar Najeriya Rice Farmers Association of Nigeria (RIFAN) da masu sarrafa shinkafa a ofishinsa dake Abuja.

Gwamnatin tarayya ta ware kudi na mussaman domin karya farashin shinkafa yar gida
Gwamnatin tarayya ta ware kudi na mussaman domin karya farashin shinkafa yar gida
Asali: Depositphotos

Ya kuma yabama kungiyar RIFAN kan jajircewarsu wajen tabbatar da ganin kasar ta cimma nasarori ta fannin samar da shinkafa.

KU KARANTA KUMA: Bani da labarin ficewar Dogara daga APC – Abubakar

Akan fasa kauri, ministan yayi bayanin cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gana da Shugaban kasar jumhuriyar Benin sannan kuma cewa suna tattaunawa wajen rage lamarin.

Ya bayar da tabbacin cewa za’a samar da maslaha na din-din-din.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel