Uban Leah ya roki gwamnatin tarayya ta bbiya diyyarta don ceto ta

Uban Leah ya roki gwamnatin tarayya ta bbiya diyyarta don ceto ta

- Gwamnatin ta taimaka don ceto diyata

- An sace ta ne tun a watan Fabrairu

- Rayuwar su na cikin hatsari

Uban Leah ya roki gwamnatin tarayya ta bbiya diyyarta don ceto ta
Uban Leah ya roki gwamnatin tarayya ta bbiya diyyarta don ceto ta
Asali: Depositphotos

A ranar 19 ga watan Fabrairu ne hankula suka tashi, sakamakon sace yammatan makarantar gwamnati dake garin dapchi, a jihar Yobe.

Bayan wata daya ne suka sako 104 daga cikin daliban, biyar sun rasa rayukan su amma Leah na hannun su sakamakon rashin barin addinin ta.

Hakan ya jawo cece ku ce a Najeriya da kasashen ketare.

Yan ta'addan sunyi barazanar kashe Leah Sharibu in dai gwamnati bata sasanta dasu ba.

Kamar yanda Mista Sharibu ya fada, Gwamnatin tarayya yakamata tayi wani abu akan hakan domin su sako diyata.

DUBA WANNAN: Sabuwar jam'iyya

Mista Sharibu ya roki yan Najeriya dasu taimaka gurin kira ga Gwamnatin tarayya da ta taimaka gurin karbo diyar shi.

Su dai Boko Haram, sun dogara da malamai da suka basu damar sace yaran jama'a da bautar dasu kamar yadda aka yi a zamanin da a Saudiyya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel