Sabuwar badakala: PDP ta ce an karkatar da kudin jirgin Nigeria Air don yakin zaben Buhari a 2019

Sabuwar badakala: PDP ta ce an karkatar da kudin jirgin Nigeria Air don yakin zaben Buhari a 2019

- Jam'iyyar PDP ta bukaci Buhari ya gaggauta kama Sanata Hadi Sirika, tare da tuhumarsa akan damfarar Nigeria zunzurutun kudi har N1.2bn

- Ta yi zargin cewa an karkatar da kudaden jirgin na Nigeria Air don gudanar da yakin zaben tazarcen Buhari a 2019

- A cewar PDP, tun a watan Yuli ta gargadi mutane akan cewa jirgin Nigeria Air bai wanzu ba, kawai makirci ne irin na gwamnati

Jam'iyyar PDP ta bukaci gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da ta gaggauta kama Ministan sufurin jiragen sama, Sanata Hadi Sirika, tare da tuhumarsa akan amfani da jirgin saman da bai wanzu ba wajen damfarar Nigeria zunzurutun kudi har N1.2bn.

PDP wacce ta bayyana wannan bukatar a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun sakataren watsa labarai na jam'iyyar na kasa Kola Ologbondiyan, ta ce ya zamawar Buhari tilas ya fito ya kare kansa akan wannan badakalar.

Ta yi zargin cewa an karkatar da kudaden jirgin na Nigeria Air don gudanar da yakin zaben tazarcen Buhari a 2019.

KARANTA WANNAN: Duk da barazanar amfani da bindiga: Yan Shi'a sun gunar da zanga zanga a Abuja

Sanarwar ta ce dakatar da shirin samar da jirgin na Nigeria Air, na daga cikin makircin gwamnatin Buhari na yin sama da fadi da dukiyar kasa, wanda ta ce makircin ba zai yi tasiri ba tun da dai jirgin bai wanzu a doron kasa ba.

Sabuwar badakala: PDP ta ce an karkatar da kudin jirgin Nigeria Air don yakin zaben Buhari a 2019
Sabuwar badakala: PDP ta ce an karkatar da kudin jirgin Nigeria Air don yakin zaben Buhari a 2019
Asali: Twitter

A cewar PDP, tun a watan Yuli ta gargadi mutane akan cewa jirgin Nigeria Air bai wanzu ba, kawai makirci ne irin na gwamnati don ta karkatar da kudin, sai ga shi tun ba a je ko ina ba gaskiya ta bayyana.

"Zuwa yanzu yan Nigeria sun san dalilin da ya sa gwamnati ta yi gaggawar zuwa Landan don gabatar da zanunkan jirage da kuma tambari na hanyoyi da filinsa, wanda ko kusa a zahiri babu wadannan abubuwa da suka zana, babu jirgin, babu lasisi, babu wani aiki na zahiri da zai nuna cewa jirgin ya wanzu.

"Da wannan ya kamata duniya ta san cewa gwamnatin Buhari gwamnati ce ta cin hanci da rashawa, da kuma gazawa wajen yaki da cin hanci kasancewar masu almundahana na cikin gwamnatin. Wannan na daga cikin babban dalilin da ya jefa tattalin arzikin kasar ya durkushe, wanda ya sa masu saka hannun jari a kasashen ketare ke tsoron sanyawa a Nigeria." a cewar PDP.

Daga karshe PDP ta bukaci da a gaggauta maido da N1.2bn na shirin samar da jirgin, da kuma gaggauta fara bincike a ma'aikatar sufurin jirage ta kasar, wanda ya hada da kudaden fansho da aka hana wasu tsoffin ma'aikatan ma'aikatar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel