Tawagar wani babban Malamin jahar Kaduna ta kai ziyara fadar shugaban kasa (Hotuna)

Tawagar wani babban Malamin jahar Kaduna ta kai ziyara fadar shugaban kasa (Hotuna)

Babban malamin addinin Musulunci daga jahar Kaduna, kuma babban limamin masallacin Al-manar dake unguwar rimi cikin garin Kaduna, Sheikh Tukur Al-Manar ya kai ziyarar ban girma ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar gwamnati dake Abuja.

Legit.ng ta ruwaito babban Malamin da kansa ya daura hotunan ziyarar daya kai ma shugaba Buhari a ailla tare da wasu abokan tafiyarsa su hudu.

KU KARANTA: Gwamna Ganduje ya gargadi sabon mataimakinsa kan abinda dayake bukata daga wajensa

Tawagar wani babban Malamin jahar Kaduna ta kai ziyara fadar shugaban kasa (Hotuna)
Ziyarar
Asali: Facebook

Tawagar Al-Manar ta kai wannan ziyara ne a ranar Lahadin data gabata, 17 ga watan Satumbar shekarar 2018 wanda ta yi daidai da 7 ga watan Muharram shekara 1440 da yin hijira kamar yadda Malamin ya bayyana.

Sheikh Al-Manar ya tabbatar da cewa sun samu shugaban kasa Buhari cikin koshin lafiya, walwala da nishadi, sa’annan yayi fatan Allah yayi ma shugaba Buhari jagora, albarka da kuma kariya daga dukkan sharrin mai sharri.

Tawagar wani babban Malamin jahar Kaduna ta kai ziyara fadar shugaban kasa (Hotuna)
Ziyarar
Asali: Facebook

“A jiya Lahadi 17/09/2018 , 7/1/1440H, muka kaiwa Shugaban kasa ziyarar ban-girma. Alhamdu lillah yana cikin koshina lafiya da nishadi. Allah Ya masa jagora da Albarka da hazaka da kariya daga dukkan sharri da makiya.” Inji Malam.

Daga karshe Malam Al-manar yayi fata Allah Ya baiwa Najeriya da al’ummar Najeriya zaman lafiya da karuwar arziki, muma anan muna cewa Amin summa Amin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng