Buhari da Shugabanni 87 za su gabatar da jawabai a taron Majalisar 'Dinkin Duniya

Buhari da Shugabanni 87 za su gabatar da jawabai a taron Majalisar 'Dinkin Duniya

Za ku ji cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari, na daya daga cikin jerin shugabannin kasashen duniya 88 da za su gabatar da jawabai a taron majalisar dinkin duniya da a za a gudanar can kasar Amurka a ranar 25 ga watan Satumba.

Shugabannin kasashen 88 za su gabatar da jawabansu daya bayan daya yayin taron da za a gudanar cikin birnin New York na kasar Amurka kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito.

A baya can an kayyade shugaba Buhari a matsayin shugaban kasa na 20 cikin jeranton shugabannin da za su gabatar da jawabansu yayin taron majalisar karo na 73 da za a gudanar a nahiyyar ta Turai.

Sai dai kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya bayar da tabbacin cewa, a halin yanzu shugaba Buhari yana kan mataki na 18 cikin jeranton shugabannin bayan an sauya fasali da tsarin gabatar da jawaban.

Buhari da Shugabanni 87 za su gabatar da jawabai a taron Majalisar 'Dinkin Duniya
Buhari da Shugabanni 87 za su gabatar da jawabai a taron Majalisar 'Dinkin Duniya
Asali: Depositphotos

Rahotanni sun bayyana cewa, shugaba Buhari zai gabatar da jawabansa gabanin shugabannin kasar Japan da kuma ta Birtaniya a ranar farko ta muhawara a tsakaninsu da za gudanar da misalin karfe 7.00 zuwa 8.00 daidai da lokacin kasar Amurka.

Legit.ng ta fahimci cewa, wannan lokaci ya yi daidai da karfe 12.00 na dare a nan Najeriya, inda shugaban kasar Brazil zai kasance shugaba na farko da zai fara bude taron da jawaban sa yayin da na kasar Amurka zai biyo bayansa bisa al'ada kasancewar kasar sa ce mai masaukin baki.

KARANTA KUMA: 'Yan Arewa ba su da wata fargaba kan sauya fasalin kasa - Makarfi

Kakakin majalisar dinkin duniya, Stephane Dujarric, ya bayyana cewa adadin shugabannin kasashen duniya da za su halarci wannan taro a shekarar nan ta 2018 sun dara na shekarar da ta gabata.

Kazalika, babban sakataren majalisar, Antonio Guterres, ya yi tsokaci kan cewa taron a wannan karo zai tattauna kan muhimman al'amurra da suka hadar da zaman lafiya, kawo karshen talauci da kuma dakile zaman kashe wando a tsakankanin matasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel