Da duminsa: Rikici ya barke yayin muzaharar Ashura a Zaria, an harbi mutum daya

Da duminsa: Rikici ya barke yayin muzaharar Ashura a Zaria, an harbi mutum daya

Labarin da ke shigo mana yanzu na nuna cewa rikici ya barke a garin Zaria, jihar Kaduna yayinda mabiya Sheik Ibrahim Zakzaky suka kusa kammala muzahar Ashura da suka saba kowani ranan irin ta yau a shekara.

Rahoton ya nuna cewa yan Shi'a sun kammala muzaharar an yi addua'r watsewa sai jami'an yan sanda suka fara harbin barkonon tsohuwa cikin jama'a wanda ya tayar da hankalin jama'an garin.

Majiyar ta kara da cewa yan sandan sun kara da harbin harsasai masu rai wanda ya sabbaba raunatan daya daga cikin yan Shi'an a kafa.

Da duminsa: Rikici ya barke yayin muzaharar Ashura a Zaria, an harbi mutum daya
Da duminsa: Rikici ya barke yayin muzaharar Ashura a Zaria, an harbi mutum daya
Asali: Facebook

Gwamnatin jihar Kaduna ta haramta wani ganawar jama'a musamman na yan Shi'a a fadin jihar. Hakan ya biyo bayan rikicin da ya barke tsakanin yan Shi'a da jami'an sojoji a ranan 12 ga watan Disamba 2015.

Da duminsa: Rikici ya barke yayin muzaharar Ashura a Zaria, an harbi mutum daya
Da duminsa: Rikici ya barke yayin muzaharar Ashura a Zaria, an harbi mutum daya
Asali: Facebook

Har ila yau, hukuma na cigaba da tsare shugaba kungiyar Shi'a, Ibrahim Zakzaky, bayan damke shi a shekarar 2015.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel