Kwastam sunyi babban kamu a Gombe inda suka wace tramadol da Diazepam na N7m

Kwastam sunyi babban kamu a Gombe inda suka wace tramadol da Diazepam na N7m

Jami’an hukumar kwastam na Najeriya, a Bauchi sun kai mamaya wani dakin ajiyan yan kasuwa a jihar Gombe inda suka kama magunguna na naira miliyan bakwai.

Kwanturolan yankin Zone D, Peters Olugboyega, ya bayyana hakan yinda yake mika magungunan ga hukumar kula a hana shan miyagun kayoyi, a hedkwatar rundunar dake Bauchi.

Ya sanar da masu kawo rahoto cewa hukumar ta kwace kwalaye 840 na Tramadol da kuma pakitin Diazepam da kudinsu ya kai kimanin N7, 350, 000.

Kwastam sunyi babban kamu a Gombe inda suka wace tramadol da Diazepam na N7m
Kwastam sunyi babban kamu a Gombe inda suka wace tramadol da Diazepam na N7m
Asali: Facebook

Olugboyega ya bayyana cewa an kama mai laifin ne a lokacin mamayar kuma yana a tsare.

A cewarsa magungunan na maye ne da ka iya taba kwakwalwa.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Jami'an hukumar hana fasa kwauri ta kasa sun kama wadansu kayayyaki wadanda adadin kudinsu ya kai sama da Naira biliyan 1 a cikin kasa da wata daya.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar yan Najeriya dake zaune a kasar Amurka sun bukaci a bari su biya kudinfansar Leah Sharibu

Babban jami'in hukumar mai kula da shiyya ta daya Mohammed Uba ne ya sanarwa da manema labarai hakan a jiya Talata, a Ikeja da ke jihar Lagos.

Ya kara da cewa bayan nasarar damke wadannan kayayyakin hukumar ta sake kama wadansu motoci na alfarma guda 17.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel