Jahiliyya: An gano wata kabila a Najeriya da har yanzu ke sayar da ‘ya’ya mata

Jahiliyya: An gano wata kabila a Najeriya da har yanzu ke sayar da ‘ya’ya mata

- A zamanin baya kafin zuwan addinai da wayewar kai, ana daukan haihuwar diya mace tamkar wata annoba

- Amma abun mamaki, sai ga shi an samu wata kabila da ake kira Becheve, a Najeriya, da har yanzu suke cinikayya da ‘ya’ya mata

- A kabilar ta Becheve, uba kan siyar da diyarsa mace ko kuma ya bayar da ita a matsayin biyan bashi ga mutumin dake binsa bashi

An samu wata kabila da ake kira “Becheve” a karamar hukumar Obanliku dake jihar Kuros Riba a kudancin Najeriya da har yanzu suke sayar da ‘ya’ya mata ko musayarsu domin biyan bashi.

Kabilar Becheve tayi suna a jihar Kuros Riba wajen yiwa ‘ya’ya mata dake da karancin shekaru auren dole.

A wani faifan bidiyo da sashen yada labarai na BBC ya saki a shafinsa, wasu daga cikin irin wadanda suka tsinci kansu cikin irin wannan mawuyacin hali sun bayyana irin halin damuwa da bakincikin da suka shiga bayan sayar da su ko kuma yin kyauta ko biyan bashi da su.

Jahiliyya: An gano wata kabila a Najeriya da har yanzu ke sayar da ‘ya’ya mata
Gwamnan jihar Kuros Riba, Farfesa Ben Ayade
Asali: Facebook

Da take bayyana irin taskun da ta tsinci kanta, Dorothy, daya daga cikin irin yaran da suka tsinci rayuwar cikin wanna muguwar al’ada, ta bayyana said a jama’a suka taru don rike ta domin wanda aka bawa ita ya sadu da ita. Dorothy ta samu juna biyu kafin ta cika shekara 12 da haihuwa.

Kazalika wata yarinya, Happines, mai shekara 14 da wani tsoho mai jikoki ya say eta tare da mayar da ita matar sa duk da ba karancin shekarunta.

DUBA WANNAN: Duk kanwar ja ce: Tsohon shugaban PDP da ya fita daga APC ya bayyana matsalar jam'iyyun

Happiness ta bayyana yadda dattijon ke lakada mata duka tare da tuna mata cewar kudinsa ya saka ya sayo ta.

Wani malamin addinin Kirista, Fasto Akonam Richards, maza a kabilar ta Becheve na da ikon yin duk yadda suka so da yarinyar da suka saya ko aka basu a matsayin biyan.

Sannan ya kara da cewar yanzu haka sun fara ceto wasu daga cikin irin wadannan yara tare da ganin sun kawo karshen wannan bakar al’ada da tuni duniya ta dade da dainawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel