Fulani sun bukaci gwamnatin tarayya ta raba Makiyaya da Makamai

Fulani sun bukaci gwamnatin tarayya ta raba Makiyaya da Makamai

Mun samu rahoton cewa, Fulani sun mika kokon bararsu akan gwamnatin jiha da ta tarayya su hada gwiwa da juna wajen raba makiyaya da makamai sakamakon zarginsu da kai munanan hare-hare na ta'addanci.

Lamidon Zugobia dake karamar hukumar Guri ta jihar Jigawa, Isa Adamu, shine ya mika wannan muhimmiyar bukata ta neman gwamnatin jihar da ta kuma ta tarayya akan su gaggauta magance wannan annoba a da ta hana su sakat.

Mista Adamau kamar yadda shafin jaridar Daily Nigerian ya ruwaito, ya mika wannan koko na bara yayin ganawa da dukkanin masu rauwa da tsaki da kwamitin sulhu tsakanin makiyaya da manoma ya gudanar a ranar Talatar da ta gabata.

Fulani sun bukaci gwamnatin tarayya ta raba Makiyaya da Makamai
Fulani sun bukaci gwamnatin tarayya ta raba Makiyaya da Makamai
Asali: Depositphotos

A cewar sam makiyaya dauke da makamai daga yankin Arewacin jihar Bauchi na ci gaba da kutsowa yankunansu inda suke lalata gonaki tare da zartar hare-hare kan al'ummarsu ba tare da wani hakki ba.

KARANTA KUMA: Aukuwar wani hari ta salwantar da rayukan Mutane 4 a jihar Filato

Legit.ng ta fahimci cewa, a sanadiyar haka ne ya sanya Mallam Adamu ke kira ga gwamnati akan ta yi gaggawar raba makiyaya da makamai domin samun kwanciyar hankali da kuma zaman lafiya a yankunan su.

Kazalika ya kuma jaddada zargin cewa rikici tsakanin makiyaya da manoma na aukuwa ne a sanadiyar wata boyayyar manufa daga bangaren makiyaya sabanin yadda ake ikirari na cewar rashin wuraren kiwo ke haddasa shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel