Kansiloli guda 10 sun lashi takobin tsige shugaban karamar hukuma akan laifuka 8

Kansiloli guda 10 sun lashi takobin tsige shugaban karamar hukuma akan laifuka 8

A yanzu haka cikin shugaban karamar hukumar Yawuri ta jahar Jebbi, Alhaji Musa Muhammad Stone ya duri ruwa biyo bayan tsigewa dayake fuskanta daga wasu kansilolinsa guda goma da suka hade masa kai, inji rahoton Rariya.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan bahallatsa ta faru ne sakamakon tsatstsamar dangantaka data shiga tsakanin shugaban karamar hukumar da kansilolin, inda suka zarginsa da yin kaca kaca da kundin tsarin mulki, don haka suka ga dacewar yin awon gaba da shi.

KU KARANTA: Gwamonin APC 13 sun raka Buhari zuwa jahar Osun a shirin zaben gwamnan jahar

Kansiloli guda 10 sun lashi takobin tsige shugaban karamar hukuma akan laifuka 8
Takardar
Asali: Depositphotos

Kansilolin su goma sun hada ne da Alhassan Adamu, Ahmad Adamu, Abdullahi Adamu Tondi, Shehu Umar, Murtala Sale, Husai Muhammad, Rashidu Kasimu, Atiku Isiyaku da Rayyanu Waziri, kuma tuni suka rattafa hannaye kan takardar tsige shugaban nasu.

Kansilolin karamar hukumar Yawurin su goma a karkashin jagorancin Kansila Shehu Umar sun bayyana laifuka guda bakwai da suke zargin shugaban karamar hukumar da tafkawa kamar haka:

1- Rashin zama karamar hukumarsa domin jin korafe korafe talakawansa

2- Kin gudanar da aikin hanyar lokos da aka ware masa kudi naira million hudu da dubu dari hudu

3- Rashin kyakkyawar alaka da talakawansa

4- Yin kacakaca da dokokin aikin gwamnati

5- Gwamnati ta bada naira milliyan daya da dubu Aba mallamai addini amma yabasu dubu dari biyu.

6- Gwamnati ta bada kudi aba malaman zabe wato Inec domin ayi ma mutane rejista amma bai basu ba.

7- Kashe naira milyan uku da dubu dari biyar na (over head code) ba bisa ka'ida ba.

8- Gwamnati ta ware kudi domin gyaran mototocin karamar hukumar Tiffer hilux bulldozer amma ya sayarda motocin batare da yin gyaranba.

A yanzu ana nan ana tsumayin yadda zata kaya a wannan bahallatsa tsakanin shugaban karamar hukumar Yawuri da kansilolinsa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel