Gwamnati ta rufe gonar Obasanjo

Gwamnati ta rufe gonar Obasanjo

- An kule daya daga cikin kamfanin tsohon shugaban kasa, Cif Obasanjo da ke jihar Oyo

- Gwamnatin jihar ta kule Obasanjo Farms ne tare da wasu kamfanoni 15 ne saboda sun ki biyan haraji

- Gwamnatin ta ce ba za ta bude kamfanonin ba har sai lokacin da suka biya gwamnatin jihar hakokinta

A yau, Talata 18 ga watan Satumba ne gwamnatin Jihar Oyo ta kule gonar tsohon shugaban kasa, Obasanjo da wasu kamfanoni 15 a jihar saboda rashin biyan kudin haraji ga hukumar kulawa da muhalli na jihar.

Jami'an sashin sanya ido na hukumomin jihar karkashin jagorancin hukumar karbar haraji na jihar me suka kule kamfanonin.

Gwamnati ta rufe gonar Obasanjo
Gwamnati ta rufe gonar Obasanjo
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Mai gadi ya nemi al'auransa ya rasa bayan karbar kudin dan siyasa

Sauran kamfanonin da aka rufe sun hada da Black Horse, Heinemann Educational Books, Lister Flour Mills, Evans Brother, Butterfield bakery, Chicken Republic, MRS oil da Rasmed Publicity.

Ciyaman din hukumar, Bicci Ali, ya shaidawa manema labarai cewa ya zama dole a dauki mataki a kan kamfanonin saboda sun ki bin umurnin hukumar na biyan harajinsu duk da sakonni na tuni da akayi ta aike musu a baya.

Ya ce, "Munyi tattaki zuwa harabar wasu kamfanoni da suka ki biyan gwamnatin jihar Oyo hakkinta na haraji bayan mun tunatar da su har ma da lika takardun gargadi a ofishoshinsu amma hakan bai sa sun biya ba.

"Hakan ya sa muka tafi harabar kamfanonin muka kulle, muka hana kowa shiga har sai lokacin da su kayi biyaya ga dokar jihar kafin mu bude."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel