Yanzu Yanzu: Sultan da shugaban CAN sun kulla yarjejeniyar zaman lafiya kafin zaben 2019

Yanzu Yanzu: Sultan da shugaban CAN sun kulla yarjejeniyar zaman lafiya kafin zaben 2019

- Sultan na Sokoto, Alhaji Sa’ad Abubakar III da shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya, Rev. Samson Ayokunle, sun kulla yarjejeniyar zaman lafiya

- Sun shiga yarjejeniyar ne domin tabbatar da zaman lafiya kafin, lokaci da kuma bayan zaben 2019

- Shugabannin sun bukaci Musulmai da Kiristoci da su cigaaba da aiki tare, su guje ma rikici, sannan su rungumi sasanci da jajircewa wajen gina kasa mai aminci da amana

Sultan na Sokoto, Alhaji Sa’ad Abubakar III da shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya, Rev. Samson Ayokunle, sun kulla yarjejeniyar zaman lafiya domin tabbatar da zaman lafiya kafin, lokaci da kuma bayan zaben 2019.

Sun kulla yarjejeniyar ne a babban birnin tarayya, Abuja a ranar Talata, 18 ga watan Satumba.

Sultan ya samu wakilcin sarkin Keffi, Dr Shehu Chindo-Yamusa, yayinda shugaban kungiyar CAN ya samu wakilcin shugaban cocin of Methodist Church, Rev. Samuel Uche.

Yanzu Yanzu: Sultan da shugaban CAN sun kulla yarjejeniyar zaman lafiya kafin zaben 2019
Yanzu Yanzu: Sultan da shugaban CAN sun kulla yarjejeniyar zaman lafiya kafin zaben 2019
Asali: Facebook

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa an sanya hannu a yarjejeniyar zaman lafiyan ne a wani taron kaddamar da zaman lafiya wanda kungiyar addinai na Najeriya wato Nigerian Interfaith Action Association (NIFAA) tare da hain gwiwar wasu hukumomin cikin gida da na waje suka shirya.

KU KARANTA KUMA: 2019: Babban jigon APC a Sokoto ya sauya sheka zuwa PDP

Shugabannin biyu sun bukaci Musulmai da Kiristoci da su cigaaba da aiki tare, su guje ma rikici, sannan su rungumi sasanci da jajircewa wajen gina kasa mai aminci da amana.

Sun sha alwashin tabbatar da zabe mai inganci bisa tafarkin damokradiyya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel