Gwamonin APC 13 sun raka Buhari zuwa jahar Osun a shirin zaben gwamnan jahar

Gwamonin APC 13 sun raka Buhari zuwa jahar Osun a shirin zaben gwamnan jahar

A ranar Talata, 18 ga watan Satumba ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa babban birnin jahar Osun, Osogbo don halartar babban gangamin yakin neman zaben dan takarar gwamnan jahar na jam’iyyar APC.

Buhari ya halarci wannan gangami ne don mara ma dan takarar jam’iyyar APC a zaben gwamnan jahar dake karatowa, Isiaka Oyetola, tsohon shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jahar Osun.

Legit.ng ta ruwaito sai da Buhari ya fara sauka a filin sauka da tashin jirage dake garin Ibadan na jahar Oyo inda gwamnan jahar, Isiaka Abiola Ajimobi ya tarbe shi, kafin daga nan ya wuce garin Osogbon jahar Osun inda gwamnan jahar Rauf Aregbesola ya tarbe shi.

KU KARANTA: Jama’an kasar Afirka ta kudu sun cika da farin ciki yayin da gwamnati ta halasta shan tabar wiwi

Rahotanni sun tabbatar da cewar an yi gangami da aka dade ba taba hada kamarsa ba a Osun, wanda ya samu halartar shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomole, jagoran APC, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, tsohon shugaban APC Bisi Akande.

Gwamonin APC 13 sun raka Buhari zuwa jahar Osun a shirin zaben gwamnan jahar
Buhari
Asali: Depositphotos

Haka zalika an hangi keyar wasu gwamnonin jam’iyyar APC da suka hada da na Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, na Zamfara, Abdul Aziz Yari, na Kano Abdullahi Ganduje, Legas Akinwumi Ambode, Filato Simon Lalong, Kebbi Atiku Bagudu, Ogun Ibikunle Amosun.

Sauran gwamnonin sun hada da gwamnan jahar Ondo,Rotimi Akeredolu, da zababben gwamnan jahar Ekiti Kayode Fayemi, na Borno Kashim Shettima, na Neja Abubakar Sanin a da kuma gwamnan jahar Edo Obaseki.

Bugu da kari taron ya samu halartar ministocin Najeriya da sauran jiga jigan yayan jamiyyar APC da dama, inda aka jiyo Buhari na rokan jama’an jahar dasu zabi Oyetola saboda ya shirya tsaf don cigaba da aiki daga inda gwamna Rauf ya tsaya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel