Daga fara aiki sabuwar ministan kudi ta gano wata babbar kalubale da Najeriya ke fuskanta

Daga fara aiki sabuwar ministan kudi ta gano wata babbar kalubale da Najeriya ke fuskanta

Sabuwar ministan wucin gadi a ma’aikatar kudin Najeriya, Hajiya Zainab Shamsuna Ahmad ta bayyana ta babbar matsala da gwamnatin Najeriya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ke fuskanta daya kunshi, inji rahoton gidan talabijin na Channels.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito minstan ta bayyana wannan kalubale a matsayin karancin kudaden shiga na gwamnatin tarayya, inda ta bada tabbacin ma’aikatar kudi a karkashin sa idonta zata habbaka adadin kudaden shiga da gwamnati ke samu.

KU KARANTA: Mutane 3,487 sun samu dubu biyar biyar na Baba Buhari a karamar hukuma daya ta Jahar Jigawa

Ministar ta bayyana haka ne a ranar Litinin, 17 ga watan Satumba ranar data kama aiki a matsayin sabuwar ministar kudi, inda tace: “Muna fuskantar babbar kalubale, kuma ya rage namu mu tabbata mun kara inganta kudaden dake shigo ma Gwamnati.

“Shugaban kasa ya yarda damu matuka cewa zamu iya wannan aiki idan harm un hada kai da junanmu, wannan aikin zai amfani yan kasa gabaki daya.” Inji ta, sa’annan ta dauki alwashin yin aiki tukuru don ganin ta daidaita tattalin arzikin kasar nan.

Hajiya Zainab ta yi kira ga ma’aikatan dasu tabbata basu baiwa shugaban kasa kunya ba, sakamakon amincewar da yayi musu. Shima a nasa jawabin, babban sakataren ma’aikatan, Mahmus Isa Dutse ya tabbatar da bada hadin kai ga ministan.

Kafin wannan sabon mukamin, Zainab Shamsuna Ahmad ta kasance karamar ministar kasafi da tsare tsare, amma Buhari ya nadata wannan mukamin biyo bayan murabus da tsohuwar ministan kudi, Kemi Adeosun ta yi sakamakon amfani da takardar NYSC na bogi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel