Rashin adalci ke ci gaba da haddasa ta'addanci a Najeriya - Lamido

Rashin adalci ke ci gaba da haddasa ta'addanci a Najeriya - Lamido

A ranar Litinin din da ta gabata ne tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya yi zargin cewa ci gaba da aukuwar ta'addanci musamman zubar jini da kuma garkuwa da mutane na kara ta'azzara ne a sakamakon tsanani na rashin adalci a kasar nan.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, tsohon gwamnan ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai jim kadan bayan ganawarsa da kungiyar shugabannin Kudancin Najeriya a daular shugaban kabilar Ijaw, Cif Edwin Clark, dake babban birnin kasar nan na tarayya.

Yake cewa, "al'adu da dabi'un gudanar da harkokin gwamnati sun tabarbare a sanadiyar tsabar rashin adalci da ya yi tsananin gaske a kasar nan wanda a bisa tsari ya kamaci kowace gwamnati ta bai wa muhimmanci."

Rashin adalci ke haddasa ta'addanci a Najeriya - Lamido
Rashin adalci ke haddasa ta'addanci a Najeriya - Lamido
Asali: Facebook

"Wannan shine babban dalilin yake kara hura wuta kan ta'azzarar ta'addancin musamman garkuwa da mutane, hare-haren Boko Haram, kashe-kashe cikin jihohin Taraba, Adamawa, Zamfara da kuma Sakkwato."

Ya ci gaba da cewa, "ana gudanar da tsarin shugabanci a kasar nan ba tare da wata doka ba, da a sanadiyar haka al'ummar Najeriya tuni suka dawo daga rakiyar wannan gwamnati mai cike da zalunci gami da rashin adalci."

Rahotanni sun bayyana cewa, tsohon gwamnan ya kausasa harshensa gami da bayyana takaicin sa dangane da yadda gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ke gurbata duk wani tanadi na ingantattun tsare-tsare da gwamnatocin baya suka shimfida a kasar nan.

KARANTA KUMA: 2019: Jam'iyyar PDP za ta yiwa 'yan takararta 13 bincike na titsiye a ranar Alhamis

Iren-iren tsaffin shugabannin kasar nan da tsohon gwamnan ya hikaito dangane da yadda shugaba Buhari ya yi watsi da akidun su na kishin kasar nan sun hadar da; Tafawa Balewa, Obafemi Awolow, Aminu Kano, Nnamdi Azikwe da kuma Sardauna, Ahmadu Bello.

Kazalika tsohon gwamnan ya bayyana takaicin sa gami da da na sanin yadda shugaba Buhari ya yaudari kundin tsarin mulkin kasar nan wajen aiwatar da hidima tukuru ga yankunan da suka fi kada ma su kuri'u yayin zaben 2015.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel