Sanata Shehu Sani ya fadawa sabon Shugaban DSS Bichi hanyoyin da zai bi ya zauna lafiya

Sanata Shehu Sani ya fadawa sabon Shugaban DSS Bichi hanyoyin da zai bi ya zauna lafiya

Mun samu labari cewa wani Sanatan Majalisar Tarayya ya ba sabon Shugaban Hukumar DSS da aka nada watau Yusuf Magaji Bichi shawarwari kusan 7 da zai kula da su idan har yana so ya ci nasarar aiki a Najeriya.

Sanata Shehu Sani ya fadawa sabon Shugaban DSS Bichi hanyoyin da zai bi ya zauna lafiya
Shehu Sani ya fadawa sabon Shugaban DSS Yusuf Magaji Bichi ya bi a hankali da 'Yan siyasa
Asali: Depositphotos

Daga cikin shawarwarin da babban Sanata Shehu Sani ya ba Yusuf Magaji Bichi wanda ya shiga ofis a karshen makon jiya akwai nuna kwarewa wajen sanin aiki da kuma bin dokar kasa sau-da-kafa yadda ya kamata.

Fitaccen ‘Dan Majalisar ya kuma nemi sabon Shugaban na DSS ya kawo karshen satar jama’a da ake yi ana garkuwa da su. Shehu Sani ya kuma nemi Yusuf Bichi ya rika bin umarnin Kotu sannan ya guji shiga cikin siyasa.

KU KARANTA: Yadda aka kashe Janar Sani Abacha - Inji Al-Mustafa

Sauran shawarwarin da Sanatan ya ba shugaban na Hukumar tsaro masu fararen kaya sun hada da kawo karshen ta’addanci da kuma biyan Ma’aikatan sa hakkin su. Sanatan ya kuma nemi Bichi ya bi a hankali da ‘Yan siyasa.

A makon jiya ne Shugaban kasa Buhari ya nada sabon Shugaban Hukumar tsaro na DSS. Buhari ya nada Yusuf Magaji Bichi a matsayin wanda zai Lawal daura da aka tsige daga aiki bayan wani mamaye Majalisa da ya sa aka yi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel