2019: Jam'iyyar PDP za ta yiwa 'yan takararta 13 bincike na titsiye a ranar Alhamis

2019: Jam'iyyar PDP za ta yiwa 'yan takararta 13 bincike na titsiye a ranar Alhamis

Da sanadin bincike na jaridar The Punch mun samu rahoton cewa, kwamitin amintattu na jam'iyyar PDP zai gana da manema takarar kujerar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar domin bincike da tantancesu kan yiwuwar fidda gwani daya tilo.

Rahotan kamar yadda shafin jaridar na The Punch ta ruwaito ya bayyana cewa, kwamitin na mutum 12 bisa jagorancin Sanata Walid Jibrin, zai gudanar da wannan muhimmin aiki wajen ganawa tare da tantance 'yan tarakarar da sanyin safiyar ranar Alhamis ta wannan mako.

Majiyar rahoton ta bayyana cewa, tuni jam'iyyar ta sanar da manema takarar kujerar shugaban kasa 13 dangane da wannan lamari a ranar Litinin din da gabata.

Har ila yau, manema takara na jam'iyyar sun hadar da; tsohon mataimakin shugaban kasa; Atiku Abubakar, Gwamnan jihar Sakkwatto; Aminu Tambuwal, Gwamnan jihar Gombe; Ibrahim Dankwambo, tsohon gwamnan jihar Kano; Sanata Rabi'u Kwankwaso da kuma tsohon gwamnan jihar Sakkwato; Attahiru Bafarawa.

2019: Jam'iyyar PDP za ta yiwa 'yan takararta 13 bincike na titsiye a ranar Alhamis
2019: Jam'iyyar PDP za ta yiwa 'yan takararta 13 bincike na titsiye a ranar Alhamis
Asali: Depositphotos

Sauran manema takarar da jam'iyyar ta gayyata sun hadar da; Shugaban majalisar dattawa; Bukola Saraki, tsohon ministan ayyuka na musamman; Tanimu Turaki, tsohon gwamnan jihar Filato; Jonah Jang, tsohon gwamnan jihar Kaduna; Ahmed Makarfi da kuma tsohon shugaban majalisar dattawa; Sanata David Mark.

Kazalika sauran wadanda ake sa ran su halarci wannan taro sun hadar da; tsohon gwamnan jihar Jigawa; Alhaji Sule Lamido, Dakta Datti Baba-Ahmed dakuma Usifo Stanley.

KARANTA KUMA: Gwamnatin Tarayya ta fitar da N3bn domin magance annobar ambaliyar ruwa a Najeriya

Rahotanni sun bayyana cewa, jam'iyyar za ta gana da manema takarar domin tattauna lamarin da neman yardarsu gami da amincewa kan yiwuwar fidda gwani daya tilo da zai fafata a babban zabe na 2019.

Legit.ng ta fahimci cewa, jam'iyyar na ci gaba da kai ruwa rana tsakanin ta da manema takarar domin kulla yarjejeniya a tsakaninsu ta fidda gwani daya tilo dake da cancantar rusa soyayyar dake zukatan al'ummar Najeriya ta shugaban kasa Muhammadu Buhari musamman a Arewacin Najeriya.

A yayin haka kuma jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, akwai yiwuwar manema takarar kujerar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar ta PDP za su kulla yarjejeniya a tsakaninsu yayin zaben fidda gwani da za ta gudanar a ranakun 5 da 6 ga watan Oktoba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel