Rikici ya barke a jam'iyyar APC a Bauchi

Rikici ya barke a jam'iyyar APC a Bauchi

Jam'iyyar All Progressives Congress babin jihar Bauchi ta afka a cikin rikici a daidai lokacin da zaben 2019 ke kara gabatowa.

Hakan na zuwa ne bayan wasu daga cikin masu so su tsaya takarar gwamna a zaben 2019 karkashin jam'iyyar sun yi zargin cewa shugabannin jam'iyyar na so su bai wa gwamnan jihar tikitin sake takara kai tsaye ba tare da zaben fitar da gwani na kato bayan kato ba.

Tsohon ministan lafiya, Dr Muhammad Pate da takwaransa na 'yan sanda, Alhaji Yakubu Lame sun bayyana cewa jam'iyyar na so ta yi musu yankan-baya, BBC Hausa ta ruwaito.

Rikici ya barke a jam'iyyar APC a Bauchi
Rikici ya barke a jam'iyyar APC a Bauchi
Asali: Depositphotos

Dr Pate ya yi kira ga shugaban jam'iyyar na kasa baki daya, Adams Oshiomhole da ya dauki mataki domin gyaro wannan matsala da ta kunno kai.

Sai dai shugaban jam'iyyar APC na jihar Bauchi Alhaji Uba Nana ya ce sun dauki matakin yin zabe na wakilai ne domin a zauna lafiya.

KU KARANTA KUMA: Tawagar shahararren dan sanda Abba Kyari sunyi gagarumin nasara

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa hukumar kuma tallata hajoji a jihar Kwara tayi barazanar cire allunan tallar duk wani dan siyasa a jihar da bai biya kudaden haraji ga hukumar ba.

Shugaban hukumar, Ahmed Olufadi, ne ya sanar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) yau, Litinin, a Ilorin, babban birnin jihar Kwara.

Sai dai wasu magoya bayan jam’iyyar APC sun ce gwamnatin jihar na son fakewa da sunan haraji domin hana ‘yan takaarar ta kafa fastoci da tallata kansu a manyan biranen jihar.

Sai dai Olufadi ya bayyana cewar fiye da kashi 90 na allunan tallar ‘yan siyasa a jihar ba bisa ka’ida da doka aka kafa su ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku nme mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel