Alhaji ya yanke jiki ya fadi a gaban jirgi a Makka ranar dawowarsa

Alhaji ya yanke jiki ya fadi a gaban jirgi a Makka ranar dawowarsa

- Wani Alhaji dan jihar Katsina ya rasu a Saudiyya

- Alhajin ya yanke jiki ya fadi ne a filin tashin jiragen sama kafin ya shiga jirgi

- An garzaya da shi asbiti nan take amma daga baya ya ce ga garinku

Wani Alhajin Jihar Katsina mai suna Abdullahi Adamu Damuna, ya yanke jiki ya fadi a yayin da ya ke hanyarsa ta shiga jirgin dawowa gida a filin tashin jirage na Jeddah a yau Litinin.

Damuna, wanda dan asalin karamar hukumar Kusada ne ya yanke jiki ya fadi ne a wajen da jami'an Kwastam suka kammala duba kayayakinsa kamar yadda muka samu daga Daily Trust.

Alhaji ya yanke jiki ya fadi a gaban jirgi a Makka ranar dawowarsa
Alhaji ya yanke jiki ya fadi a gaban jirgi a Makka ranar dawowarsa
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Mai gadi ya nemi al'auransa ya rasa bayan karbar kudin dan siyasa

An garzaya da Damuna asibiti amma likitoci daga baya sun sanar da cewa ya riga mu gidan gaskiya.

Wani shaidan ganin ido ya ce hankullan mahajjata ya tashi a yayin da suka zagaye shi domin taimaka masa kafin a tafi dashi asibiti.

Jami'an hukumar aikin hajji na jihar Katsina ba su sanar da rasuwarsa ba amma wani jami'in hukumar da ya nemi a boye sunansa ya tabbatar da afkuwar lamarin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel