Sanatoci 10 da komawarsu majalisar dattawa ke da wuya

Sanatoci 10 da komawarsu majalisar dattawa ke da wuya

Yayinda yake shirin zaben shugaban kasa, gwamnoni, sanatoci, yan majalisan wakilai da majalisa dokokin jihohi, Legit.ng ta kawo muku yan majalisar dattawa goma da kujerarsu ke rawa bisa ga irin dambarwan siyasan da ke faruwa tsakaninsu.

Ga jerinsu:

1. Ubale Shittu

Kujerar Sanata Ubale Shittu mai wakiltan Jigawa ta yamma ya fara rawa ne tun lokacin da ya sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa ta PDP tare da Saraki.

2. Rabiu Musa Kwankwaso

Duk da cewa ya bayyana niyyar takara kujeran shugaban kasa, rahotanni sun nuna cewa takardan takara biyu yan takaran PDP suka saya; na shugaban kasa da na Sanata. Sunyi hakan ne domin takara kujerar sanata idan suka fadi a zaben fitar da gwamnin jam’iyyar PDP. Amma da alamun lokacin haka ya kure ga Kwankwaso saboda abokin hamayyarsa Malam Ibrahim Shekarau ya shirya tsaf domin maye gurbinsa a majaliar dattaawa.

3. Sanata Kabiru Marafa

Bayan kwashe shekaru yana fito-na-fito da gwamna Abdulaziz Yari, sanata Marafa ya bayyana niyyar takara kujeran gwamnan karkashin jam’iyyar APC. Da alamun zai yi biyu babu bisa ga irin karfin da gwamna Yari ke dashi a jihar ta Zamfara.

KU KARANTA: Babu wanda ya isa ya tsige ni – Saraki

4. Sanata Hunkuyi

Bayan adawan da suka buga da gwamnan jihar, Sanata Suleiman Usman Hunkuyi, ya sauya sheka daga APC da aka zabesa zuwa jam’iyyar PDP. Sanna ya bayyana niyyar takara kujerar gwamnan jihar.

5. Sanata Rafiu Ibrahim

Duk da goyon bayan da yake nunawa maigidansu Bukola Saraki, da alamun ba za’a dama da shi a 2019 ba tun da gwamnan jihar Kwara, Fatai Ahmed, ya alanta niyyar kwace kujerarsa a majalisar dattawa.

6. Sanata Ahmed Sani Yarima

Domin nuna girma da dattaku, Sanata Sani Yarima, ya yafe kujerarsa ga gwamna AbdulAziz Yari, wanda ya bayyana niyyar takara kujeran.

7. Sanata Kabiru Gaya

Bayan cin mutuncin da akayi masa a jihar Kano kwanakin baya da kuma goyon bayan da jama’a ke nunawa Hanarbul Kau Sumaila, da alamun cewa komawa majalisar dattawan Kabiru Gaya na rawa.

8. Sanata Shehu Sani

Duk da cewa ya ki sauya sheka daga jam’iyyar APC, gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’I, ya bayyana cewa ba zai bari Shehu Sani ya koma majalisa ba. Tuni yayi masa kishiya a cikin gida.

9. Sanata Danjuma Laah

Bayan irin rikicin da sukayi da gwamnan jihar, Sanata mai wakiltar Kaduna ta kudu na da wuyan komawa majalisa dubi ga cewa mataimakin gwamnan jihar Kaduna, Barnabas Bantex, ya alanta niyyar kwace kujeransa.

10. Sanata Isa Misau

Abubuwa sun cabewa sanata Isa Misau tun bayan sauya shekarsa jam’iyyar PDP. Jama’ar Misau sun fito kwansu da kwarkwatarsu domin nuna bacin ransu da irin wannan adawa da yakeyi ga shugaba Buhari, hakan ya sanya komawarsa majalisa ke da wuya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel