Jam’iyyar APC ta barke a dalilin wanda za a tsaida Gwamna a Sokoto

Jam’iyyar APC ta barke a dalilin wanda za a tsaida Gwamna a Sokoto

Mun samu labari daga Daily Nigerian cewa cewa rigimar wanda zai gaje kujerar Aminu Waziri Tambuwal a Sokoto ta fara fitowa fili bayan rikici ya fara barkewa a Jam’iyyar APC mai mulki.

Jam’iyyar APC ta barke a dalilin wanda za a tsaida Gwamna a Sokoto
Wammako na so APC ta tsaida Mataimakin Tambuwal Gwamna a 2019
Asali: Depositphotos

DAILY NIGERIAN ta rahoto cewa an fara samun rikici a cikin Jam’iyyar APC ne bayan da tsohon Gwamna Aliyu Magatakarda Wammako ya nuna cewa ya fasa daura wani fitaccen tsohon Kwamishinan sa yayi takarar Gwamna a 2019.

A baya tsohon Gwamnan Jihar na Sokoto Aliyu Wammako yayi tunanin kakaba Farouk Yabo wanda ya taba yi masa Kwamishinan kudi a matsayin ‘Dan takarar APC a zaben 2019. Sai dai yanzu Sanatan yayi wuf ya sake shawara.

Ana tunanin cewa wasu na-kusa da Sanatan ne su ka zuga shi yayi watsi da Faruk Yabo ya fara tunanin dauko Mataimakin Gwamna Tambuwal watau Ahmed Aliyu a matsayin wanda zai rikewa Jam’iyyar APC tuta a Sokoto a zaben 2019.

KU KARANTA: Mu mu ka yi sanadiyyar da Jonathan ya hau mulki - Tambuwal

Yanzu haka dai ‘Dan Majalisar da ke wakiltar Kware da Wammako watau Hon. Ahmed Kalambaina da Shugaban APC na Sokoto Isah Sadiq Acida duk su na tare da Faruk Yabo a maimakon wanda Wammako din ya ke so ya tsaida takara.

‘Yan Majalisar dokokin Jihar Sokoto da-dama su na bayan tsohon Kwamishinan kudin Jihar inda har su ka saya masa fam din takara. Mafi yawan ‘Yan APC dai ba za su yi wa Wammako biyayya ba idan ya zabi Aliyu inji wani ‘Dan siyasa.

Faruk Malami Yabo wanda ya rike Kwamishinan kudi da kuma na kananan Hukumomi a baya ya soki Gwamna Tambuwal kwanaki inda yace sam Gwamnan wanda yanzu yaje neman kujerar Shugaban kasa a PDP bai da hangen nesa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel