Yan sanda sun yi magana game da dan siyasar da aka kama yana wanka da jini

Yan sanda sun yi magana game da dan siyasar da aka kama yana wanka da jini

- Yan sandan Najeriya sun yi magana kan dan siyasar da aka kama yana wanka da jini

- Sunce damfarar sa matasan suka yi

- Sun ce tuni har sun fara kama wasu daga cikin su

Dazu ne dai muka kawo maku labarin wani dan majalisar jiha da wasu matasa a jihar Osun dake a shiyyar kudu maso yammacin Najeriya suka cafke su dake zaman shugaban masu rinjaye a majalisar jiha Honorabul Timothy Owoeye yana wanka a tsirara cikin jeji.

Yan sanda sun yi magana game da dan siyasar da aka kama yana wanka da jini
Yan sanda sun yi magana game da dan siyasar da aka kama yana wanka da jini
Asali: Twitter

Shi dai shugaban masu rinjaye a majalisar jiha Honorabul Timothy Owoeye, an ce wankan da aka kama shi yana yi baya rasa nasaba da tsafi irin na 'yan tsubbu da kan sa 'yan siyasa yi musamman ma ganin zabukan 2019 na kara karatowa.

Kawo yanzu dai mun samu karin bayani daga jami'an yan sandan jihar inda suka ce lamarin ya faru ne kimanin watanni shida da suka gabata sannan kuma tuni har sun fara cafke wasu daga cikin matasan da suka tozarta dan majalisar.

Yan sandan sun cigaba da cewa gadar zare ce aka shiryawa dan majalisar tare da hadin bakin wasu masu magnin gargajiya wadanda suka umurci dan majalisar da ya je yayi wanka tsirara domin samun nasara a siyasar sa.

Suka cigaba da cewa yan tsibbun haka zalika sai suka hada kai da wasu mutane inda suka zo suka dauki hotunan dan majalisar yana wanka sannan kuma suka bukaci ya rika basu kudi akai akai idan dai baya so su tona masa asiri.

Legit.ng dai ta samu cewa matasan sun dauki hoto da bidiyon dan majalisar yana tsakiyar wanka da jinin ne suka kama shi duk da dai kawo yanzu ba'a tabbatar da jinin mutane ne ba ko kuwa na dabba.

Da dan majalisar dai yaga dubun tasa ta cika shine ya baiwa matasan makudan kudade domin su rufa masa asiri amma daga baya kuma suka fallasa maganar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel