Da dumin sa: Jirgin kasa yayi hadari daga Abuja zuwa Kaduna, ya kashe wata mata
- Jirgin kasa yayi hadari daga Abuja zuwa Kaduna
- Ya kashe wata mata akan hanyar sa
- A kwanan baya ma jirgin ya kashe shanu 50
Jirgin kasan dake jigilar fasinjoji daga garin Abuja zuwa Kaduna a ranar Asabar yayi hadari kan hanyar sa daga garin Abuja zuwa Kaduna jim kadan bayan barin tashar sa dake a unguwar Idu, Kubuwa, birnin tarayya Abuja.

Asali: Depositphotos
KU KARANTA: An yi wa Buhari ca game da nade-naden sa
Majiyar mu dai ta tabbatar mana da cewa jirgin kasan dai haka zalika ya yi raga-raga da wata baiwar Allah inda ya markade ta ta yadda ba ma a gane ta kwata-kwata.
Legit.ng ta samu cewa a kwanan baya ma dai jirgin kasan yayi hatsari akan hanyar ta sa ta zuwa Abuja a cikin daji inda ya kashe akalla shanu sama hamsin na fulani suna tsakar kiwo.
A wani labarin kuma, Hafsan sojojin saman Najeriya Sadiq Abubakar ya bayyana cewa rundunar sa ta sayi akalla jiragen yaki talatin tun bayan hawan shugaba Muhammadu Buhari a karagar mulki kimanin shekaru uku da suka shude.
Hafsan sojin dai ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a yayin bude wasu muhimman ayyuka a makarantar koyon aikin sojan saman ta Najeriya dake a garin Kaduna.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng