An gano dan majalisa da ya yi karyar ya kashe N41m domin gina wajen horas da matasa

An gano dan majalisa da ya yi karyar ya kashe N41m domin gina wajen horas da matasa

- An samu wani dan majalisar wakilai na tarayya, Muhammad Umar Jega, da laifin karyar aikin N41 miliyan

- Mr Muhammad Umar Jega, daga jihar Kebbi ya yi ikirarin gina cibiyar matasa a garin Jega amma an neme ta an rasa

- Mazauna garin da kuma kungiyar Tracka duk sun tabbatar da cewa babu inda aka gina wannan cibiyar a Jega

Wata kungiya mai zaman kanta da ke bibiyar ayyukan ma'aikatan gwamnati a Najeriya, Tracka, ta gano karyar da dan majalisa tarayya daga jihar Kebbi, Mr Muhammad Umar Jega, ya yi na cewa ya gina Cibiyar Koyar da matasa ayyuka kan kudi N41 miliyan.

Muhammad Umar Jega shine ke wakiltan mazabun Gwandu/Aliero/Jega a majalisar wakilai ta tarayya kamar yadda West Africa Reporters ta ruwaito.

An gano dan majalisa da ya yi karyar ya kashe N41m domin gina wajen horas da matasa
An gano dan majalisa da ya yi karyar ya kashe N41m domin gina wajen horas da matasa
Asali: Instagram

A shekarar 2017, Jega ya ware zunzurutun kudi N41 miliyan a matsayin kudin aikin raya mazabansa, inda ya ce zaiyi amfani da kudin wajen gina Cibiyar horas da matasa sana'o'i a garin Jega amma da Tracka da ziyarci garin ba'a ga aikin ba.

DUBA WANNAN: Muhimman abubuwa 8 da ya kamata ku sani game da sabuwar Ministan Kudi, Zainab Ahmed

Wakilin Tracka da ke jihar Kebbi, Mr Emmanuel Yaro ya ce babu wata Cibiyar horas da matasa sana'o'i a garin Jega kamar yadda Sanatan ya fadi.

Wani mazaunin garin Jega, Mr. Dalhatu ya ce mazauna garin Jega suna fushi saboda rashin gudanar da aikin da dan majalisar baiyi ba duk da cewa an ware kudin aikin da sunansu.

Wani lauya mazaunin Jega, Awalu Jega, ya ce rashin bayyana inda a kayi aikin yana daya daga cikin hanyoyin da wasu 'yan siyasa ke amfani dashi suna karkatar da kudaden talakawa.

Jagoran Tracka, Mr. Uadamen Illevbaoje, ya ce dan majalisar ya gaza bayar da bayyanin inda aikin ya ke. Kafar West Africa Reporters da tayi kokarin jin ta bakin 'dan majalisar amma ba'a same shi a waya ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel