Sanata David Mark ya ziyarci tsohon Shugaban kasa, IBB, a birnin Minna

Sanata David Mark ya ziyarci tsohon Shugaban kasa, IBB, a birnin Minna

Mun samu rahoton cewa tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata David Mark, ya kai ziyara birnin Minna na jihar Neja inda ya yi wata ganawar sirrance da tsohon shugaban kasar Najeriya na mulkin soji, Ibrahim Badamasi Babangida.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, ganawar tsakanin jiga-jigan biyu ta gudana har na tsawon sa'o'i biyu a katafaren gida mallakin tsohon sojin dake birnin na Minna.

David Mark, wanda ya isa jihar da misalin karfe 1.30 na tsakar ranar yau ta Asabar, ya ziyarci tsohon shugaban kasar cikin tawagar sa ta da kunshi Sanata Zainab Kure, Sanata Tunde Ogbeha da kuma Sanata Suleiman Adokwe.

Rahotanni sun bayyana cewa, Sanata Mark wanda ya kasance a majalisar dattawa tun a shekarar 1999, na daya daga cikin jiga-jigan manema takarar kujerar shugaban kasa da suka ziyarci tsohon sojin domin neman goyon bayan sa kan manufar da suka sanya a gaba.

Sauran manema takarar kujerar shugaban kasa da suka ziyarci tsohon shugaban kasar sun hadar da; shugaban majalisar dattawa; Abubakar Bukola Saraki da tsohon mataimakin shugaban kasa; Alhaji Atiku Abubakar.

Sauran wandanda suka ziyarci tsohon shugaban kasar sun hadar da; tsohon gwamnan jihar Sakkwato; Attahiru Bafarawa, tsohon gwamnan jihar Jigawa; Alhaji Sule Lamido da kuma tsohon gwamnan jihar Kaduna; Ahmed Makarfi.

KARANTA KUMA: 2019: Dalilin da zai sanya dole a sake zaben Buhari - Mamman Idris

Legit.ng ta fahimci cewa, dukkanin masu hankoron kujerar ta shugaban kasa da suka ziyarci Babangida na fafata takarar su ne a karkashin jam'iyyar adawa ta PDP.

A yayin ganawar daya daga cikin 'yan tawagar tsohon shugaban majalisar ta dattawa da manema labarai, Sanata Zainab Kure, ta kirayi daukacin al'ummar Najeriya da dukkanin masu ruwa da tsaki akan su tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali yayin gudanar da zaben 2019.\

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel