Ran maza ya baci: Kauraye da maharba sun bazama dazukan Zamfara domin farutar ‘yan boindiga, hotuna
Yanzu haka hadakar kungiyoyin ‘yan tauri da maharba daga jihohin Sokoto da Zamfara sun ruguntsuma sun shiga daji, bayan kammala shirin yakin, domin farautar ‘yan b indigar da suka dade suna kai hare-hare tare da garkuwa da mutane a sassan jihohin biyu.
A cikin hotunan da ake yadawa a dandalin sada zumunta, an ga ‘yan taurin da maharban na bi garuruwa, a babbar mota (Kanta), domin diban sanannun ‘yan tauri da maharba da zasu shiga dazuka domin farautar ‘yan bindigar.
Duk kokarin gwamnati na kawo karshen aiyukan ta’addancin ‘yan bindigar bai haifar da sakamakon da ake so ba, don kuwa har yanzu ‘yan bindigar na cigaba da kai hare-hare tare da kashe mutane ko yin garkuwa da su ko kuma yi masu fashin dukiyoyi.

Asali: Facebook

Asali: Facebook
Ko a ranar Alhamis da ta gabata said a jaridar Legit.ng ta kawo maku labarin cewar ‘yan bindiga sun kashe mutane 13 tare da raunata wasu da dama a wani hari da suka kai kauyen Badarawa da ke karamar Shinkafi a jihar Zamfara.
DUBA WANNAN: Buhari zai halarci bikin rufe tseren Dawakai a Katsina
Daily Nigerian ta ruwaito cewa 'yan bindigar sun far ma kauyen ne da safiyar ranar ta Alhamis inda suka rika harbin dukkan wanda suka hadu dashi kuma daga baya suka rika bi gidajen mutane daukan abinda suke so.

Asali: Facebook

Asali: Facebook
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng