Zaben 2019: INEC za ta haramtawa masu kad'a kuri'a amfani da wayoyi a rumfunan zabe

Zaben 2019: INEC za ta haramtawa masu kad'a kuri'a amfani da wayoyi a rumfunan zabe

- Hukumar INEC ta ce za ta haramtawa mutane zuwa da manyan wayoyi a rumfunan zabe don dakile siyen kuri'u

- INEC ta bayyana cewa mafi akasarin masu zuwa da wayoyi a akwatunan zabe, na amfani da su ne wajen daukar hoto, don zama shaida ga masu sayen kuri'un

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, Mahmood Yakubu ya ce hukumar na duba yiyuwar haramta amfani da wayar salula a rumfunan zabe. Wannan mataki na daga cikin shirye shiryen gudanar da sahihin zabe a 2019.

Mr. Yakubu ya bayyana hakan a ranar Juma'a, a wani taron musayar ra'ayi kan gudanar da zabe, wanda wata kungiyar fararen hula ta shirya, mai suna YIAGA'S Watching Thevote, a otel din Sharaton da ke Abuja.

Ya bayyana cewa za'a karbi wayoyin masu kada kuri'a da zaran sun amshi takardun jefa kuri'arsu a akwatunan zabensu, don magance matsalar siyen kuri'u.

Shugaban hukumar INEC, Mr. Yakubu
Shugaban hukumar INEC, Mr. Yakubu
Asali: Depositphotos

KARANTA WANNAN: Sabuwar doka: An haramtawa jami'an yan sanda karin matsayi har sai sun zana jarabawa

"Hukumar zata yi lokarin haramta amfani da wayar salula da wasu na'urori da zasu iya zama hanyar siyen kuri'u a ranar danake gudanar da zabe" a cewar Mr. Yakubu.

Hukumar ta INEC ta bayyana cewa mafi akasarin masu zuwa da wayoyi a akwatunan zabe, na amfani da su ne wajen daukar hoto, don zama shaida ga masu sayen kuri'un.

"Kowa ya san cewa, mafi akasarin masu zuwa kada kuri'a da wayar salula, na zuwa da su ne don daukar hoton takardar kada kuri'arsu bayan sun dangwalawa jam'iyyar da suke so, daga baya sai su nunawa masu sayen kuri'un, don zama shaidar sun zabi wanda aka ce su zaba.

"Akwai yiyuwar zamu haramtawa masu manyan wayoyi zuwa da wayoyinsu idan sun zo kada kuri'a a akwatunan zaben su, don dakile siyen kuri'u" a cewar shugaban hukumar ta INEC.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel