Fitaccen Malamin addini Gumi ya ba mutanen Najeriya shawara game da shugabanci

Fitaccen Malamin addini Gumi ya ba mutanen Najeriya shawara game da shugabanci

Mun samu labari cewa babban Malamin addinin Musulunci Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi yayi wani jawabi a wajen bude wata Makaranta da Ambasada Dalhatu Sarki Tafida ya gina a Kaduna.

Fitaccen Malamin addini Gumi ya ba mutanen Najeriya shawara game da shugabanci
Gumi yace ana bukatar mutum mai kuzari ya mulki Najeriya
Asali: Depositphotos

Babban Malamin Musuluncin ya fadakar da shugabannin kasar nan cewa dole akwai bukatar su rika karbar shawara daga Jama’a. Malamin yace har manyan Annabawan Allah sai da Ubangiji ya nemi su rika jin ta bakin sauran Mabiyan su.

Shehin Malamin ya kuma yi kira ga Mutane cewa Manzon Allah yace Shugabanni za su yi nadamar kwadayin mulki da su kayi a Ranar lahira. Malamin yace ana so a zabi wadanda su ka cancanta sai dai ba a son mutum ya kwallafawa ran sa.

Malamin ya kuma bayyana cewa dole Jama’a su rika zaben wadanda su ka cika siffofin shugabanci domin su ja ragamar su. Daga cikin siffofin, Gumi yace ana son shugaba mai hakuri da tausayi da afuwa da kauda kai da lallashi da jawo jama’a.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya bayyana irin nasarorin da ya samu a Gwamnati

Kwararren Masanin ya kuma bayyana cewa idan har Shugaba ba ya karbar shawara, za a gamu da matsaloli a ban kasa. Sheikh Gumi ya kuma tunatar da jama’a cewa shugabanci amana ce kuma dole a zabi wanda ya kware ko da ba a kaunar sa.

Babban Masanin na addini Dr. hmad Abubakar Mahmud Gumi ya kuma yi kira ga Jama’a su daina rikici kan siyasa domin banbancin ra’ayin Jam’iyya. Bajimin Malamin ya kuma ba jama’a shawara su guji aibanta juna domin gudun Ubangiji ya fallasa su.

Idan ba ku manta ba a jiya ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada sabon Shugaban Hukumar tsaro na DSS. Hakan dai ya jawo suka musamman daga bangaren Kudancin Kasar nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng