Duk kanwar ja ce: Idan har PDP barayi ne to APC ma barayi ne - Lamido

Duk kanwar ja ce: Idan har PDP barayi ne to APC ma barayi ne - Lamido

- Dr Sule Lamido ya yi kira ga al'umar Nigeria da su hada hannu wajen kawo karshen mulkin shugaban kasa Buhari da jam'iyyar APC

- Ya ce PDP da aka tsana yau dai sune suka cika APC, idan har za'a kira PDP barayi, to shuwagabannin da ke zaune a Abuja ma barayi ne

- Sule Lamido ya bayyan cewa Nigeria ta kowa ce, ba wai ta APC, Lamido ko PDP ba, don haka babu wanda ya isa ya zo ya tarwatsa kasar

Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Dr Sule Lamido ya yi kira ga al'umar Nigeria da su hada hannu da jam'iyyar sa wajen kawo karshen mulkin kama karya da shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da jam'iyyar APC ke yi a kasar.

Lamido wanda ya yi ikirarin cewa har yanzu Buhari bai canja halinsa ba, duba da kitsa tuggun juyin mulki da ya yi a 1983, inda ya murkushe gwamnatin farar hula tare da garkame yan siyasar lokacin a kurkuku, "Wannan Buharin sai shine har yanzu, gashi nan yana azabtar da mutane"

Tsohon gwamnan jihar Jigawa wanda ya bayyana hakan jiya a Benin City, a lokacin da ya ke zantawa da wakilan PDP da ke kada kuri'ar zaben fitar da gwani na jihar Edo, a shirye shiryen fuskantar zaben fitar da gwani na jam'iyyar da zai gudana a cikin watan Oktoba.

Duk kanwar ja ce: Idan har PDP barayi ne to APC ma barayi ne - Lamido
Duk kanwar ja ce: Idan har PDP barayi ne to APC ma barayi ne - Lamido
Asali: Depositphotos

KARANTA WANNAN: Buhari ya bukaci yan Nigeria su zabi APC don gujewa kuskuren 1999 zuwa 2015

Ya ce: "Tabbas PDP ta tabka wasu kira kurai a baya, wasu daga cikin yayan jam'iyyar sun gudanar da lamuransu ba dai dai ba, amma dai mutane ne, da yawan mu na kiran sunan Buhari, kamar wani ubangijin bayi.

"Tattalin arzikin kasar ya karye, babu tsaro, babu wasu hukumomi da zasu kare mu idan aka zo yin adalci da mulkin gaskiya. Amma ace wai mutum daya zai zo yana juya kasar kamar tashi ce shi kadai. A yau jam'iyyar da ake cewa zata canja komai, ta koma jam'iyyar azzalumai, sai yunwa, bacin rai da kuncin rayuwa suka jefa mutane.

"Idan an hankalta da kyau, za'a ga cewa yayan jam'iyyar PDzp ne suka koma cikin APC. Sune tsofaffin gwamnoni, sanatoci, ministoci, jakadu da dai sauransu. PDP da aka tsana yau dai sune suka cika APC, idan har kunce mana barayi, to shuwagabannin da ke zaune a Abuja ma barayi ne.

"Nigeria tamu ce gaba daya, ba wai ta APC, Lamido ko PDP ba, don haka babu wanda ya isa ya zo ya tarwatsa kasar. Kowa ya sani, halin da kasar ta ke a ciki ba'a fuskance shi a mulkin PDP ba, sai a mulkin APC." a cewar Sule Lamido.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel