Kwankwaso ya kai wa Janar Ibrahim Babangida ziyara a gida

Kwankwaso ya kai wa Janar Ibrahim Babangida ziyara a gida

Mun samu labari cewa Sanatan Kano ta tsakiya Rabiu Kwankwaso ya zauna da tsohon Shugaban kasar Najeriya Janar Ibrahim Badamasi Babangida a gidan sa da ke cikin Garin Minna a Neja.

Kwankwaso ya kai wa Janar Ibrahim Babangida ziyara a gida
Kwankwaso ya sa labule da Janar Babangida a gidan sa Hotuna daga Saifullahi Hasan
Asali: Depositphotos

'Dan takarar Shugaban kasar a karkashin Jam’iyyar PDP ya leka Jihar Neja inda yake cigaba da yakin neman zaben fitar da gwani a babban Jam’iyyar adawar kasar. Rabi'u Kwankwaso ya gana da manyan PDP na Jihar Neja.

Kwankwaso ya zauna da shugabannin PDP na kasa da ke Jihar ta Neja sannan kuma ya gana da kwamitin amintattu na Jam’iyyar da kuma sauran ‘Ya ‘yan Jam’iyyar da za su tsaida ‘Dan takarar Shugaban kasa a zaben 2019.

KU KARANTA: Kwankwaso ya bugi gaba game da zaben 2019

Tsohon Gwamnan na Kano yayi amfani da wannan dama wajen kai wa tsohon Shugaban kasa a lokacin mulkin Soji watau Janar Ibrahim Babangida ziyara har gidan sa da ke Yankin Hilltop Mansion a cikin babban Garin Minna.

Wani Hadimin babban Sanatan ya bayyana mana cewa Kwankwaso da mutanen na sa sun kai wa tsohon Shugaban kuma daya daga cikin manyan PDP ziyarar girma. IBB dai yana cikin Dattawan da ake ji da su yanzu a kasar nan.

Shekaran iya kun ji cewa ‘Yan takaran PDP za su hada kai wajen tika Buhari da kasa a 2019. Kwankwaso ya nemi masu harin kujerar Shugaban kasar su hada karfi da karfe wajen kifar da APC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng