Sojojin Najeriya sun yi fata-fata da 'yan bindiga 10, mai satar mutane a Kaduna

Sojojin Najeriya sun yi fata-fata da 'yan bindiga 10, mai satar mutane a Kaduna

- Sojojin Najeriya sun yi fata-fata da 'yan bindiga 10, mai satar mutane a Kaduna

- Sun kashe su ne a kananan hukumomin Chikun da Birnin Gwari

Jami'an sojojin Najeriya na runduna ta daya dake a jihar Kaduna a ranar Alhamis ta sanar da samun nasarar yin fata-fata da akalla wasu da ake zargin 'yan bindiga ne su goma da kuma kama wani mai satar mutane daya a kananan hukumomin Chikun da Birnin Gwari, jihar Kaduna.

Sojojin Najeriya sun yi fata-fata da 'yan bindiga 10, mai satar mutane a Kaduna
Sojojin Najeriya sun yi fata-fata da 'yan bindiga 10, mai satar mutane a Kaduna
Asali: Facebook

KU KARANTA: 'Yan kasuwa sun kunyata Gwamna El-rufai

Mataimakin daraktan hulda da jama'a na rundunar ne dai mai suna Kanal Muhammad Dole shine ya sanar da hakan a cikin wata takardar manema labarai da ya rabawa a garin Kaduna.

Legit.ng ta samu cewa Kanal Muhammad Dole a cikin takardar sanarwar ta sa ya bayyana cewa akalla 'yan bindigar shida ne suka kashe a kauyukan Kidandan akan hanyar Dogon Dawa, Unguwar Bilya, Sofa da Unguwan Nakuli dukkan su a cu=ikin karamar hukumar Birnin Gwari daga 10 ga watan Satumba.

Haka zalika yace sauran wadanda jami'an sojojin suka yi fata-fata da su din sune a kauyukan Kidan Isa, Gidan Haruna Mobale da kuma Kuduru yayin da wasu kuma suka tsere da raunuka da dama a jikin su.

A wani labarin kuma, jami'an sojojin saman Najeriya dake a cikin rundunar hadin gwuiwa ta Lafiya Dole dake yaki da 'yan ta'addan Boko Haram a shiyyar Arewa maso gabashin kasar nan sun sanar da samun gagarumar nasara a kan 'yan ta'addan a maboyar su dake a dajin Sambisa.

Kamar yadda muka smu, rundunar ta bayyana cewa ta samu yin galaba akan 'yan ta'addan ne tare kuma da yin fata-fata da ma'ajiyar makaman a dajin na Sambisa dake zaman mafaka gare su.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel