APC ta bayyana abinda zai faru da Dogara idan ya koma PDP

APC ta bayyana abinda zai faru da Dogara idan ya koma PDP

- Jam'iyyar APC tayi tsokaci kan jita-jitar sauya sheka zuwa PDP da ake Kakakin Majalisa Yakubu Dogara ya yi

- Jam'iyyar ta ce labarin sauya shekar bai bata mamaki ba saboda irin tayar da kayar baya da Dogara keyi a APC

- APC ta tabbatarwa Dogara cewa zai sha mummunan kaye muddin ya yi takarar majalisa karkashin wata jam'iyyar adawa

APC ta bayyana abinda zai faru da Dogara idan ya koma PDP
APC ta bayyana abinda zai faru da Dogara idan ya koma PDP
Asali: Twitter

Jam'iyyar APC ta shawarci Kakakin Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara da kada ya sake ya ce zai yi takarar a 2019 karkashin inuwar jam'iyyar adawa ta PDP domin zai sha mummunar kaye ne.

A yayin da yake tsokaci kan jita-jitar cewa Kakakin Majalisar zai sauya sheka zuwa PDP, Mukadashin Sakataren Shirye-Shirye na APC, Yekini Nabena ya ce ba zaiyi mamaki ba idan Dogara ya koma PDP saboda irin zagon kasa da ya keyi a APC.

DUBA WANNAN: Magoya bayan Dogara sun saya masa tikikin takara ta jam'iyyar PDP

Ya ce tayar da kayan bayan na Dogara ya karu musamman bayan da jam'iyyar PDP ta lashe zabe a karamar hukumarsa ta Bogoro a zaben kujerar Sanata da aka yi a jihar Bauchi cikin kwanakin nan.

"Mun samu rahotanni daga wasu kafafen yada labarai cewa, Kakakin majalisar walilai na tarayya, Yakubu Dogara, na jam'iyyar APC ya sauya sheka zuwa wata jam'iyyar adawa," inji Nabena.

"Labarin ficewar Dogara bai bamu mamaki ba saboda dama mun lura da irin tayar da kayan baya da ya keyi da hadin baki da shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya yi amfani da dukkan damar da ya ke dashi domin kawo cikas a APC.

"Muna bawa Dogara shawarar cewa mudin ya ce zaiyi takarar kujerar Majalisa karkashin jam'iyyar adawa tabbas ya sani cewa zai sha kaye," inji Nabena.

A wani rahoton, Legit.ng ta kawo muku cewa wasu magoya bayan Dogara sun kai masa fam din takarar ta jam'iyyar PDP suna rokonsa ya dawo PDP saboda sun lura ana yi masa rashin adalci a APC.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel