Bai kamata ace Najeriya ce tafi kowa matalauta a duniya ba - Tsohon shugaban Najeriya

Bai kamata ace Najeriya ce tafi kowa matalauta a duniya ba - Tsohon shugaban Najeriya

- Tsohon shugaba kasa, Olusegun Obasanjo, ya koka kan yadda abubuwa suka tabarbare a Najeriya har ta zama kasar da tafi talauci a duniya

- Obasanjo ya ce akwai kasashen da su kafi Najeriya yawan mutane kamar India amma duk da hakan mun fi su talauci

- Obasanjo ya ce dole dukkan jam'iyyun Najeriya da jama'a su hada kai domin kawo canji da zai kawar da talauci a Najeriya

Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo, ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda kididigar da akayi kwana-kwanan nan ya nuna cewa Najeriya na cikin kasashe duniya masu fama da talauci, inda ya ce hakan bai dace ba.

Obasanjo ya yi mamakin yadda kasa kamar Najeriya mai mutane misalin 180 miliyan za ta dara kasa kamar India mai mutane 1.3 biliyan talauci.

Bai dace Najeriya ta zama kasar da a kafi fama da talauci a duniya ba - Obasanjo
Bai dace Najeriya ta zama kasar da a kafi fama da talauci a duniya ba - Obasanjo
Asali: Getty Images

DUBA WANNAN: Dukkan 'yan takarar PDP sun hada kai a kan abu guda - Bafarawa

Obasanjo ya yi wannan jawabin ne a jiya Laraba a Legas yayin da shugbanin jam'iyyar Africa Democratic Congress ADC suka kai masa ziyara kamar yadda sanarwa da ta fito daga hadiminsa kan fannin yada labarai, Kehinde Akinyemi ya sanar.

"Kamar yadda kuka fada, mafi yawancin 'yan Najeriya na rayuwa cikin matsanancin hali sai dai wasu kalilan. Hakan kuke so mu cigaba da rayuwa har tsawon shekaru hudu nan gaba?

Obasanjo ya ce dole jam'iyyun siyasa su hada kansu waje guda domin PDP ko ADC kawai ba za su iya kawo canji ba, dole sai dukkan 'yan Najeriya sun hada kai waje guda.

A cikin 'yan kwanakin nan ne akayi wata kididiga da ya bayyana cewa Najeriya ce kasar da tafi fama da talauci a duniya.

"India na da mutane 1.3 biliyan, Najeriya kuma na da 180 miliyan. Amma duk da haka Najeriya ce tafi sauran kasashen talauci. A gaskiya hakan bai dace ya faru da Najeriya ba," inji Obasanjo.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel