A dai lura da kyau akwai wani kulli da Fayose ke yi tunda yace zai mika kansa ga EFCC - APC
- Jam'iyyar APC ta gargadi hukumar EFCC akan bukatar da Fayose ya nema na gabatar da kansa a gaban ta
- APC ta zargi gwamnan da wani shiri na son guduwa daga kasar ta hanyar amfani da dabara
- EFCC dai na tuhumar gwamnan mai shirin barin gado da wasu laifi
Jam’iyyar All Progressives Congress(APC) na Ekiti a ranar Laraba, 12 ga watan Satumba ta bayyana cewar da gwamna Ayodele Fayose yayi zai mika kansa ga hukumar EFCC a ranar da zai bar kujerar mulki a matsayin wani tuggu.
Jam’iyyar APC tace lallai gwamnan na kulla wani siri ne ta yadda zai samu damar guduwa daga kasar cikin sauki.

Asali: Depositphotos
Jam’iyyar ta hannun babban sakatarenlabaranta, Taiwo Olatunbosun ta dasa ayar tambaya kan dallin da yasa Fayose ya amince da Karin kasafin nairan biliyan 10 da majalisar dokoki jihar ta nema kasa da wata daya kafin saukarsa mulki.
Jam’iyyar ta bayyana shirin Fayos gurfana a gaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa a nmatsayin ci gaba mai kyau, sai dai tayi gargadin cewa hakan na iya kasancewa makirci, sanin cewa Fayose ya iya dabaru kuma yana iya shirya gadar zare ga huumar EFCC da suran hukumomin tsaro.
A baya Legit.ng ta rahoto cewa hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC za ta taso Gwamnan Ekiti Ayo Fayose a gaba.
KU KARANTA KUMA: Tursasa ni aka yi ina zaman lafiya na na shigo cikin siyasa – Buhari
EFCC ta fara kakkabe takardun ta domin fara binciken badakalar da ke kan Fayose. Tana zargin Fayose da laifuffuka da dama.
Hukumar dai tana jira ne kurum Gwamnan ya sauka daga kujerar sa ta yi ram da shi. Dokar kasa ba ta bada dama a bincike Gwamna da Shugaban kasa ba muddin su na kan mulki. Kwanan nan ne Fayosen zai mika mulkin Jihar.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng