Yanzu-yanzu: Jirgin Ali Modu Sheriff ta sabbaba kulle filin jirgin saman Abuja
1 - tsawon mintuna
An kulle babban filin jirgin saman Nnamdi Azikwe International Airport, da ke birnin tarayya Abuja bayan wata jirgin sama ta toshe hanyar wucewab jirgi.
Wanna abu ya faru ne misalin karfe 10 na daren jiya Laraba.

Asali: Facebook
Majiya mai karfi sun bayyanawa jaridar Daily Nigerian cewa jirgin kira 5N BOD Gulfstream na tsohon gwamnan jihar Borno, Ali Modu Sheriff ne.
A yanzu dai, babu jirgin da zai iya sauka a filin jirgin saman Abuja, sai dai mutum ya tafi Legas ko Kano sannan ya tafi inda yake nufi.
Zamu kawo muku cikakken rahoton...
Asali: Legit.ng