Yanzu-yanzu: Yakubu Dogara ya siya Fam na PDP ba tare da ya bar APC ba

Yanzu-yanzu: Yakubu Dogara ya siya Fam na PDP ba tare da ya bar APC ba

Kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara ya siya takardan bayyana niyyar takaran kujeran majalisar wakilai karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP, jaridar Premium Times ta samu daga majiya mai karfi.

Kakakin ya siya wannan Fam ne a yau Laraba, 12 ga watan Satumba inda dimbin magoya bayansa suka hallara a gidansa na Abuja.

Yakubu Dogara ya bayyanawa dimbin masoyansa cewa yayi niyyar barin siyasa bayan shekari 12 a majalisar wakilai kuma kakakin jam'iyya, amma bukatan jama'arsa ya wajabta masa cigaba da zama a majalisan.

"Wasu sunce zasu koremu daga siyasa, amma muna sanar musu da cewa Allah kadai da mutane zasu iya koranmu," Dogara yace da nufin martani ga gwamnan jihar, Mohammed Abubakar.

Yanzu-yanzu: Yakubu Dogara ya siya Fam na PDP ba tare da ya bar APC ba
Yanzu-yanzu: Yakubu Dogara ya siya Fam na PDP ba tare da ya bar APC ba
Asali: Depositphotos

Rikicin Yakubu Dogara da gwamnan jiharsa bai banbanta da na sauran gwamnoni APC irin Ogun, Kaduna, Jigawa da Oyo ba.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya mayar da takardan takaransa hedkwatar APC

A wadannan jihohi, yan majalisan sun sauya sheka daga APC saboda tsoron kada gwamnonin suci mutuncinsu ta hanyan juya jam'iyyar yadda suka ga dama. A jihar Kaduna ne kawai sanata Shehu Sani ya cigaba da zama a jam'iyyar duk da gaba da kiyayya.

A yanzu dai, komai ya bayyana cewa Yakubu Dogara ya bar APC.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel