Baba 'yar Karo: Labarin wata Bahaushiya da tayi gwagwarmaya tun kafin zuwan turawa

Baba 'yar Karo: Labarin wata Bahaushiya da tayi gwagwarmaya tun kafin zuwan turawa

Cinikin bayi abu ne da ya kasance ruwa dare a arewacin Najeriya a karni na 19 a lokacin turawan mulkin mallaka. So da yawa akan kai hari kauyuka daban-daban inda ake kama mutane a gonaki da gidajensu daga baya a sayar da su a matsayin bayi.

Baba wata tsohuwa ce wadda aka haife ta a 1877, a kauyen Karo da ke kusa a Azarewa a tsohuwar daular Usmaniyya wadda ta hada da Zaria da Kano. Mahaifinta manomi ne kuma yana karantar da Kur'ani.

Baba ta hadu da wata baturiya mai suna Mary Smith a 1949. Mary ta wallafa littafi a kan gwagwarmayar ruyuwar Baba 'yar Karo wanda ya zama abin nazari ga masu karantar tarihin Hausawa a zamanin mulkin mallaka.

Labarin wata tsohuwar Bahaushiya da tayi gwagwarmaya tun kafin zuwan turawa
Labarin wata tsohuwar Bahaushiya da tayi gwagwarmaya tun kafin zuwan turawa
Asali: Depositphotos

A wancan zamanin, ana ta gwabza yaki a daular ta Usmaniyya hakan yasa cinikin bayi ya zama ruwan dare. A cikin litafinta, Mary ta bayyana yadda Sarki ke bayar da umurni makada su hau tsibiri su buga gangan domin sanar da mutane cewa masu kama bayi suna zuwa kuma sai ka ga mutane suna gudu suna shigowa kofar gari domin tsira.

DUBA WANNAN: Yadda zamu yi da kudaden da muka kwato daga hannun 'yan wawaso - Buhari

An kama wasu daga cikin 'yan uwan Baba a wata sumame da aka kai sai dai daga baya an sako su bayan an biya kudi masu yawa na fansa.

"Sun kai farmaki gidan kanin mahaifina, Ubangida a tsakiyar dare. Sun sace matarsa mai juna biyu da yaransa guda uku da wasu bayinsa guda goma. Bayan kwanaki 30, mun samu labarin cewa masu satan bayin sun tafi sai mahaifinmu ya ce mu tafi gonar shinkafarsa d ake kusa da rafi," inji Baba.

Baba ta ce kullum suna cikin fargaba ne saboda kada masu sace mutane su kama su a kuma sayar da su a matsayin bayi.

Kazalika, Baba ta bayyana cewa a wannan zamanin ba'a tilastawa mata auren wadanda ba su so kuma idan mace ba ta son mijinta, tana iya neman saki ba tare da tsoron tsangwama ba. Ta ce tana da wata suruka wadda ta auri maza 11 a rayurta.

Baba bata taba haihuwa ba har ta rasu a 1951 duk da cewa da auri mazaje hudu a rayurta. Mazajen da ta aura sun hada da Duma, Mallam Maigari, Mallam Hassan da Mallam Ibrahim.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel