Ba sabun ba: Wata mace ta baiwa maza shawarar kara aure a Najeriya
- Wata mace ta baiwa maza shawarar kara aure a Najeriya
- Tace masu mace daya ya kamata su kara, masu biyu ma su kara, haka zalika masu uku ma duk kamata yayi su cike
- Tace hakan yafi dacewa akan bin 'yan matan da mazajen ke yi
Wata mace likita a babbar asibitin gwamnatin tarayya dake a garin Ebute Meta, jihar Legas tayi wani kalamin da ya dade yana yawo a kafar sadarwar zamani inda aka tsinkayi tana rokon maza da su daure su kara aure.

Asali: Facebook
KU KARANTA: Wata amarya ta haihu awa 2 kafin auren ta
Kamar dai yadda muka samu, matar ta bayyana ra'ayin ta ne a kafar sadarwar zamani inda kuma kafin kace kobo tuni maganar ta dauki hankali inda kowa ke bayyana ra'ayin sa game da batun.
Legit.ng ta samu cewa ita dai matar, mai suna Hauwa Ibrahim, ta ce tana baiwa dukkan mazan da ke da ikon kara aure to su hanzarta yin hakan.
Tace masu mace daya ya kamata su kara, masu biyu ma su kara, haka zalika masu uku ma duk kamata yayi su cike domin hakan yafi dacewa akan bin 'yan matan da mazajen ke yi.
Wannan dai na zaman tamkar wani sabon al'amari musamman ma ta yadda mata ke da tsananin kishi da adawar karin aure da mazaje kanyi.
A wani labarin kuma, Wani lamari mai cike da sarkakkiyar ban al'ajabi ya auku a garin Awo Idemili na jihar Anambara dake a shiyyar kudu maso gabashin kasar nan inda amarya ta haifi sambalelen saurayi kimanin awa biyu kafin a daura mata aure.
Ita dai amaryar mai suna Misis Chinezu Adeolisa ta bayyana wa duniya farin cikinta na samun sankacecen jariri a ranar ɗaurin aurenta da rabin ranta Mista Odeolisa.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng