An sake nada Walid Jibrin a matsayin Shugaban PDP BOT

An sake nada Walid Jibrin a matsayin Shugaban PDP BOT

Mun samu labari Jam’iyyar adawa PDP ta nada Sanata Walid Jibrin ya cigaba da aiki a matsayin Shugaban kwamitin amintattu watau BOT. Tun 2013 aka fara nada Jibrin a kan wannan mukami kafin a kara wa’adin sa kwanan nan.

An sake nada Walid Jibrin a matsayin Shugaban PDP BOT
PDP ta nada Walid Jibrin a matsayin Shugaban BOT
Asali: Depositphotos

Manyan PDP ne su ka yanke wannan hukunci bayan wani babban taro da aka yi inda aka ga dacewar a bar Walid Jibrin a kan kujerar sa. An kuma tabbatar da Sanata Adolpus Wabara a matsayin Sakataren kwamitin na BOT na PDP.

Jam’iyyar ta bada wannan sanarwa ne a makon nan inda ta kuma sanar da cewa za a fitar da ‘Dan takaran da zai iya gwabzawa da Shugaba Buhari a 2019. Yanzu dai akalla mutum 12 ne ke takarar kujerar Shugaban kasa a Jam’iyyar PDP.

KU KARANTA: Gwamnatin Jihar Kano ta bada hutun sabuwar shekara

Adolphus Wabara wanda tsohon Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya ne zai zama Mataimakin Shugaban kwamitin na BOT na tsawon shekaru 5 da aka nada. PDP dai tana kokarin kawo maslaha wajen tsaida ‘Dan takaran zaben 2019.

Dazu kun samu labari cewa ana sa rai cewa yau ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai karbi fam din sa na sake tsayawa takara a karkashin Jam’iyyar sa ta APC mai mulki a zabe mai zuwa na 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel