2019: Dasuki ya shiga tseren takarar gwamna a Gombe

2019: Dasuki ya shiga tseren takarar gwamna a Gombe

- Tsohon shugaban matasan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Alhaji Ibrahim Dasuki ya koka akan yadda Najeriya ke ci gaba da dogaro da man fetur

- Dasuki ya yanki fam din takarar gwamnan jihar Gombe a zabe mai zuwa

- Ya sha alwashin inganta fannin lafiya da ilimi idan har aka zabe shi

Alhaji Ibrahim Dasuki, tsohon shugaban matasan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, ya koka akan yadda Najeriya ke ci gaba da dogaro akan mai.

Ibrahim ya bayyana hakan a ranar Litinin, 10 ga watan Satumba a Abuja yayinda yake zantawa da manema labarai sakatariyar APC na kasa bayan ya yanki fam din takarar kujerar gwamnan Gombe a 2019.

Ya bayyana cewa dogaro da kai shine hanya guda da jihohin tarayyar kasar musamman jihohin arewa maso gabas zasu iya rike tattalin arzikinsu.

2019: Dasuki ya shiga tseren takarar gwamna a Gombe
2019: Dasuki ya shiga tseren takarar gwamna a Gombe
Asali: Depositphotos

Ya kara da cewa zai ba fannin ilimi da lafiya muhimmanci sosai sannan ya tabbatar da habbaka tattalin arzikin Gombe idan har aka zabe shi.

Yace zai tabbatar da ganin matasa sun shiga harkokin kasuwanci, inda ya kara da cewa gwamnatinsa zata mayar da hankali wajen zamanantar da harkar noma.

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa yan takara a shiyyar Kudu maso Gabas, karkashin jam'iyyar PPD, na ci gaba da nuna fushinsu a fili, sakamakon hukuncin da ofishin shiyya na jam'iyyar ya dauka, wanda suka misalta shi da kora da hali daga kudirinsu na tsayawa takara karkashin jam'iyyar.

KU KARANTA KUMA: Digiri na 3 da Gwamna Ortom ya mallaka na jabu ne – Akume

Jam'iyyar PDP a shiyyar ta bukaci yan takararta da su biya wasu kudade na daban, da suka kama daga N200,000 zuwa Miliyan biyu, don baiwa jam'iyyar damar yin gyare gyare a ofishinta na shiyya da ke Independence Layout, Enugu.

Sai dai mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa da ke a shiyyar, Deacon Austin Umahi ya ce ba wai haraji bane aka dorawa yan takarar, illa dai wasu yan kudaden shiga da jam'iyyar ta ke son tarawa don tafiyar da ayyukanta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel