Ba maganar na'urar tantance katin zabe a zaben 2019 mai zuwa - inji fadar shugaban kasa

Ba maganar na'urar tantance katin zabe a zaben 2019 mai zuwa - inji fadar shugaban kasa

- Ba maganar na'urar tantance katin zabe a zaben 2019 mai zuwa

- Fadar shugaban kasa ce tace hakan

- Fadar tace 'yan adawa ne ke yawo da maganar

Fadar shugaban kasar Najeriya karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari a ranar Litinin din da ta gabata ta bayyana cewa babu batun na'urar nan ta tantance katin zabe a cikin daftarin gyararren tsarin zaben 2018 da majalisa ta aikewa shugaban kasar.

Ba maganar na'urar tantance katin zabe a zaben 2019 mai zuwa - inji fadar shugaban kasa
Ba maganar na'urar tantance katin zabe a zaben 2019 mai zuwa - inji fadar shugaban kasa
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Ba lafiya: An nemi wani babban soja an rasa a Najeriya

Wannan ne ma dai ya sanya fadar ta ce rashin maganar na'urar da wasu 'yan matsaloli ne ma ya sa shugaba Muhammadu Buhari ya ki sanya hannu a kan kudurin dokar.

Legit.ng ta samu cewa wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da mai ba shugaban kasar shawara na musamman akan harkokin majalisar Sanata Ita Enag ya fitar ya kuma rabawa manema labarai a garin na Abuja.

Sanata Enag ya kuma kara da cewa abun takaici ne yadda wasu tsirarun 'yan adawa ke neman gogawa shugaban kasa kashi kaji game da lamarin inda suke cewa wai don akwai maganar na'urar tantancewar ne shugaban kasar ya ki sa hannu a daftarin.

A wani labarin kuma, Kamfanin sadarwar nan na MTN a Najeriya ya maka babban bankin na Najeriya watau Central Bank of Nigeria (CBN), da kuma Antoni Janar na kasar kuma ministan shari'a a gwamnatin shugaba Buhari kotu yana neman a bi masa hakkin sa.

Kamar dai yadda muka samu, shi dai kamfanin a ranar Litinin din da ta gabata ne ya shigar da karar kotu a garin Abuja, yana kalubalantar matakin da gwamnatin Najeriya ta kakaba masa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel