Da duminsa: Tsohon IG, Suleiman Abba, ya sayi fam din takarar Sanata

Da duminsa: Tsohon IG, Suleiman Abba, ya sayi fam din takarar Sanata

Tsohon rundunar 'yan sanda na kasa, Suleiman Abba, ya shiga sahun masu son jam'iyyar APC ta tsayar da su takarar Sanata a jihar Jigawa.

A yau, Litinin, ne Abba ya yanki tikitin takara a shelkwatar jam'iyyar APC na kasa dake Abuja.

Da yake ganawa da manema labarai bayan yankar katin takarar, Abba ya ce ya shiga takarar ne domin bawa jama'ar sa wakilci na gari.

Da duminsa: Tsohon IG, Suleiman Abba, ya sayi fam din takarar Sanata
Da duminsa: Tsohon IG, Suleiman Abba, ya sayi fam din takarar Sanata
Asali: Depositphotos

Abba na son jam'iyyar ta APC ne ta tsayar da shi takarar kujerar Sanatan jihar Jigawa ta tsakiya.

DUBA WANNAN: Tsohon gwamna ya sayi fam din takara daga gidan yari

Sai dai masu nazarin siyasar jihar Jigawa na ganin zai yi matukar wuya ga tsohon IG Abba ya iya kayar da Sanatan yankin, Sabo Nakudu, wanda ke daga cikin 'yan siyasa masu karfi a jam'iyyar APC a jihar Jigawa.

Baya ga Sanata Nakudu, dan tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, na neman jam'iyyar adawa ta PDP ta tsayar da shi takarar kujerar Sanatan yankin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel